logo

HAUSA

Ya kamata bangaren Amurka ya cika alkawurran da shugabanta ya dauka

2022-03-15 20:49:56 cri

A ranar 14 ga watan Maris, agogon wurin, an kara ganawar manyan jami’an Sin da Amurka a Rome, babban birnin kasar Italiya. Bangarorin biyu sun yi ganawar sahihanci, mai zurfi kuma bisa manyan tsare-tsare kan dangantakar dake tsakanin kasashensu, da muhimman batutuwan da suka shafi kasa da kasa, sun kuma amince da tabbatar da ra’ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau wajen maido da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta dace, ta samun ci gaba mai inganci da kwanciyar hankali.

A yayin ganawar, kasar Sin ta sake bayyana matsayinta kan batutuwan da suka shafi yankunan Taiwan, da Xinjiang, Tibet, da Hong Kong da dai sauransu, inda ta nuna cewa, wadannan batutuwa sun shafi muhimman muradun kasar Sin, kuma harkokin cikin gida ne na kasar, wadanda ba za’a taba yarda kasashen waje su tsoma baki a cikinsu ba. Wannan gargadi ne a bayyane kuma mai tsauri ga Amurka, sannan kuma wani jan layi ne da kasar Sin ta zana kan huldar dake tsakanin Sin da Amurka.

A yanzu haka, halin da ake ciki a kasar Ukraine, shi ne batun da ya fi daukar hankalin kasashen duniya, haka kuma a yayin ganawar da Sin da Amurka suka yi ma, an tattauna kan wannan batu. Kasar Sin ta kuduri aniyar inganta shawarwari cikin lumana, kuma a ganinta, ya kamata kasashen duniya su goyi bayan shawarwarin zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ta yadda za a kai ga cimma hakikanin nasara cikin sauri, don ganin an hanzarta sassauta halin da ake ciki.

A matsayinsa na wanda ya tada rikicin Ukraine, ya kamata bangaren Amurka ya saurari wadannan shawarwari tare da yin abubuwan da suka dace, don warware rikicin Ukraine a siyasance, maimakon yin akasin haka, ko yada labaran karya don jirkita gaskiya da neman bata sunan kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)