logo

HAUSA

Yin barci cikin awoyi 7 a ko wace rana ya fi amfana wa lafiyar mutate

2022-03-15 10:53:02 CRI

 

Kowa ya sani cewa, rashin barci ya kan raunana lafiyar mutane kwarai da gaske. Amma yin barci cikin dogon lokaci shi ma ba ya da amfani ga lafiyar mutane. Shin tsawon lokacin barci nawa ne ya fi dacewa da mutane?

Masanan ilmin likitanci sun ba mu amsa. A ganinsu, yin barci na awoyi 7 a ko wace rana ya fi amfani ga lafiyarmu.

Shehun malami Li Shunwei, wanda zaunannen wakili ne na sashen ilmin kwakwalwa na hadadiyyar kungiyar ilmin likitanci ta kasar Sin ya bayyana mana cewa, lokacin barci, wani muhimmin adadi ne da ake amfani da shi wajen tabbatar da kamuwa da ciwon rashin barci. Idan mutum bai iya yin barci cikin awoyi 6 a duk rana daya ba, to, likitoci sun tabbatar da cewa, wannan mutum ya kamu da ciwon rashin barci.

Yin barci cikin dan lokacin kadan ya kan kawo illa ga lafiyar mutane. Nazarin da aka yi ya nuna cewa, masu fama da rashin barci da yawansu ya kai kashi 80 zuwa 90 cikin dari su kan yi fama da ciwace-ciwace da dama, wadanda suka hada da ciwon zuciya, hawan jini da sauran cututtuka masu tsanani.

Mr. Li yana mai cewa, yin barci cikin dogon lokaci ko kuma cikin dan lokaci kadan su kan haifar da ciwon sukari da ciwon zuciya, har ma su kan kara wa mutane barazanar mutuwa. Yin barci cikin awoyi 7  a ko wace rana na iya rage wa masu fama da ciwon sukari da ciwon zuciya barazanar mutuwa.

Masanan da ke nazarin harkokin barci sun nuna cewa, a galibi dai akwai wasu manyan dalilai da su kan shafi barci, wato kamar cututtuka, halin da mutane suke kasancewa, matsin lambar aiki ko karatu ko kuma ta zaman rayuwa da ake fuskanta, da ma dangantakar da ke tsakanin mutane. Ga misali, ciwo ya kan yi illa kan barci, haka kuma, jarrabawa ta kan ta da hankalin dalibai, inda su iya yin barci yadda ya kamata ba.

Wasu kwararru masu ilmin abinci masu gina jiki sun ba da shawarar cewa, cin abinci masu yawa na taimakawa mutane a fannin yin barci. Madara mai zafi da ke kunshe da zuma da dabino, ko zuma, da tuffa da dai sauransu dukansu sun ba da taimako wajen yin barci yadda ya kamata. Haka kuma cin abinci masu dacewa na kyautata ingancin barci.

Mr. Li ya yi nuni da cewa, an sami wadannan sakamako ne bayan da aka yi nazari kan wasu mutane, don haka ba a iya kawar da cewa, ko da yake wasu su kan yi barci cikin awoyi 4 zuwa 5 a ko wace rana, ko kuma cikin awoyi fiye da 10, amma sai a ga suna cikin koshi lafiya.