logo

HAUSA

Sojojin Somali sun damke mayakan al-Shabab 3 a shiyyar kudancin kasar

2022-03-15 10:39:50 CRI

Rundunar sojin kasar Somali (SNA), ta ce dakarunta na musamman sun kama mayakan al-Shabab uku a ranar Litinin a yayin ayyukan samamen da suka kaddamar a shiyyar kudancin kasar Somalia.

Jami’in rundunar SNA ya fadawa gidan radiyon Mogadishu mallakin gwamnatin kasar cewa, ba a fuskanci bude wuta daga bangaren ‘yan ta’addan ba, a lokacin da sojojin suka kai samame a garin Barire da kewayensa.

Ya bayyana ta gidan radiyon cewa, an kama mutane uku, da suka hada da Abdifitah Mohamed, da Osman Omar da kuma Adan Moalim, wadanda ake zarginsu da hannu wajen shirya hare-haren bam a shiyyar.

Jami’in yace, za a mika shara’arsu ga kotun sojoji.(Ahmad)