logo

HAUSA

Malamar dake koyar da rawa ta kasar Rasha dake kokarin cimma burinta a nan kasar Sin

2022-03-14 19:47:04 CRI

A wata makarantar raye-raye dake birnin Hefei a gabashin kasar Sin, akwai wata malamar da ta fito daga kasar Rasha, wadda kuma take samun karbuwa sosai daga dalibanta. To, me ya sa wata yar kasar Rasha ta zo kasar Sin don koyar da rawa, kuma ta yaya ta cimma mafarkinta a kasar waje? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan malamar rawa ta Rasha mai suna Sophia.

Ana shirya darasin Sophia a ranar Asabar da yamma, kuma ta kan isa aji awa daya kafin zuwan dalibai, domin shirya wasu ayyuka, ciki har da bude kofa, da kwandishan da dai sauransu.

Duk da zama a kasar Sin na tsawon shekaru 14, har yanzu Sophia tana magana da Sinanci tare da alamar lafazin garinsu. Gidan Sophia yana Siberiya na kasar Rasha. Don haka ana iya tambayar dalilin da yasa ta zabi zuwa kasar Sin don zama wata malamar rawa? Sophia ta ba da amsa da cewa,

“Gidan mu yana bakin tafkin Baikal, dake Siberiya, wanda ke kusa da kasar Sin. Ban da wannan kuma, kanwar mahaifiyata tana zama a kusa da yankin Manchuria, birnin dake kan iyakar kasashen Sin da Rasha, kuma mu kan tafi gidanta, domin mu hau bas zuwa kasar Sin tare. A hakika dai, na riga na zo kasar Sin har sau da dama kafin na soma zama da aiki a nan.”

Tun tana karama, Sophia ta kan tafi kan iyakar Rasha da Sin tare da danginta, don sayen kayan yau da kullum. Don haka, kasar Sin tamkar wata makwabciyarta ce mai kirki a gare ta. Lokacin da take karatu a jami'a, Sophia ta zabi Sinanci daga cikin zababbun harsunan waje guda uku, kuma sau da yawa tana yin wasan kwaikwayo a Sin tare da tawagar wakilai.

“Yawancin dalibanmu sun zabi Sinanci, kowa ya san cewa bayan kammala karatu a jami'a, idan ba za mu iya samun aiki ba, za mu iya zuwa kasar Sin don yin aiki.”

Ta hakan, Sophia tana kara alaka da kasar Sin, kuma a karshe dai irin alakar ta sanya ta tabbatar da burinta, wato tana fatan koyar da raye-raye a kasar Sin, domin sanya mutane mafi yawa su soma kauna da koyon rawa.

A shekarar 2008, don cimma burinta, Sophia ta tafi birnin Shanghai na kasar Sin daga Rasha, kuma ta zo birnin Hefei bayan shekara guda. Ba ta taba yin tsamanin za ta yi aiki da zama a nan har tsaron shekaru 13 ba.

Domin bude dakin wasan raye-raye a kasar Sin, Sophia ta kuma dauki darussa a wuraren motsa jiki guda uku, don adana kudi na kafa makarantar koyon rawa. Bayan shekaru da yawa na aiki tukuru, a karshe Sophia ta tanadi isassun kudi na bude dakin raye-raye.

“Ina bukatar in hau keken lantarki duk rana, daga safe zuwa dare, in dauki darasi a ko wane wurin motsa jiki. Na yi ta hakan har kimanin shekaru uku, kuma na tanadin isassun kudi na bude dakin raye-raye nawa. Wuraren motsa jiki na manya ne, ba su dace da yara ba, saboda ba su da sana’a. A dakin koyon raye-raye, yara na iya samun hidimar shiga jarabawar raye-raye, da damar shiga gasa, amma ba sa iya samun irin wannan hidima a wuraren motsa jiki.”

Farkon komai yana da wahala, tun da farko dakin koyar da raye-raye na Sophia ya dauki dalibai 4 ne kawai.

Saboda kwarewarta a ba da horo na ka’in da na’in ga dalibai, Sophia tana ta samun karbuwa daga dalibai da iyayensu. Don haka, daliban dake koyon raye-raye a dakinta suna karuwa sannu da hankali, kuma adadin daliban ya karu daga guda 4 a farko zuwa fiye da 100 a yanzu.

Amma, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da ta faru ba zato ba tsamani, ta tarwatsa shirinta, har ma ta haifar da ra’ayin yin watsi da sana’arta a nan kasar Sin.

“Saboda yaduwar annobar, iyaye na suna bangaren Rasha, ni kuma ina bangaren kasar Sin, ba zan iya komawa ba, wannan ya haifar da babbar matsala. A da, yana da saukin tafiya tsakanin kasashen biyu ta jirgin sama, amma yanzu babu irin wannan damar.”

A lokacin hutu na sabuwar shekara ta 2020, Sophia ta koma kasar Rasha don ziyartar 'yan uwanta, amma saboda annobar cutar, ta kasa komowa kasar Sin, don haka ta yi ta zama a Rasha har watanni 8, hakan ya sa wasu dalibai suka dakatar da koyon raye-raye a dakinta a cikin wannan lokacin.

Sophia, wadda ba ta da tabbacin ko za ta iya komowa kasar Sin, ta taba yin tunanin yin watsi da sana’arta. Amma bayan tunani sau da yawa da ta yi, a karshe ta komo kasar Sin.

“Domin na dade ina aiki a kasar Sin, idan na koma Rasha, dole na sake fara komai daga farko, wanda hakan zai yi wahala kwarai.”

Yadda Sophia take daukar nauyin dake kanta a tsanake, ya sa dlibai da yawa sun fara kaunar ta a zuciyoyinsu.

Daliba1:

“Ina son wannan malama, saboda yadda halin koyarwarta ya bambanta da na sauran malamai, kuma ta fi ban dariya. (humor).”

Daliba2:

“A lokacin da na zo kwas din, na gano cewa, ashe malamar bakuwa ce, na yi mamaki sosai. Haka kuma, ta kware sosai kuma tana koyarwa sosai. Baya ga haka, wata bakuwa ta zo kasar Sin daga wuri mai nisa don ta koya mana yadda ake rawa, wannan ruhin yana da kyau sosai, kuma yana karfafa mana gwiwa sosai.”

Sophia ta ce, tana da wani buri, wato samu wata yariniyar dake da kwarewar rawa sosai, kuma ta yi imani da gaske cewa, wannan mafarkin zai tabbata a kasar Sin.