logo

HAUSA

“Gasar wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi mafi kyau” Ta nuna sabbin nasarorin da Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam

2022-03-14 22:21:01 CRI

“Abin da kuka yi alkawari shi ne ‘shirya gasa mai sauki, tsaro, kuma mai ban-al’ajabi’, abin da kuka yi shi ne, shirya gasa mai ban mamaki, matukar tsaro, da kuma ban-al’ajabi matuka” A yayin bikin rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 a nan birnin Beijing da aka shirya a yammacin jiya, shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na kasa da kasa, Andrew Parsons, ya yi tsokaci cewa, kasar Sin ta kafa wasu ma'aunai a wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi da kusan ya kamata a yi koyi da su a nan gaba. Kafin haka, Parsons ya bayyana karara cewa, wannan ita ce gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi “mafi kyau” da ya taba gani.

Abun da ya dace a ambata a nan shi ne, tawagar kasar Sin ta zo matsayi na farko a jerin lashe lambobin zinare da sauran lambobin yabo, lamarin da ya sa kasar Sin kafa wani sabon tarihi a fannin wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi. Wannan ya shaida yadda kasar Sin ke samun bunkasuwa sosai a fannin wasannin motsa jiki na nakasassu, kuma ya nuna irin manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam. Kamar yadda Felipe Devassa, farfesa a jami'ar URJC ta kasar Spain ya ce, "Nasarar da aka cimma ta gudanar da wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi na Beijing, ya nuna saurin bunkasuwar harkokin da suka shafi nakasassu na kasar Sin a ‘yan shekarun da suka gabata, da kuma yadda aka kiyaye muradun nakasassu yadda ya kamata.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)