logo

HAUSA

Kasar Sin ta zama zakaran gwajin dafi ga duniya a gasar Olympic

2022-03-14 21:58:09 CRI

Bisa lura da irin namijin kokarin da kwamitin da aka dorawa alhakin shiryawa da gudanar da gasar wasannin Olympic ta ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing 2022, da irin fadi-tashin da gwamnatin Sin tayi, gami da irin goyon bayan da alummun Sinawa suka bayar wajen shiryawa da kuma karbar bakuncin gasar Olympic ta lokacin sanyi da gasar ajin nakasassu, ko shakka babu, dukkan bangarorin da abin ya shafa sun cancanci yabo, musamman idan muka yi la’akari da manyan nasarorin da aka cimma tun daga farkon al’amarin har zuwa karshe.

Da maraicen ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin sanyi na kasa da kasa (IPC), Andrew Parsons, ya bayyana rufe gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 a hukumance. Koda yake, tun lokacin kaddamar da gasar a ranar 4 ga watan Maris, al’ummun kasa da kasa suna nuna kwarin gwiwar samun nasarar gasar, bisa la’akari da gagarumar nasarar da kwamitin shirya gasar Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 da ta gudana a karshen watan Fabarairu. Da ma dai masu hikimar magana na cewa, “Juma’ar da zata yi kyau, daga Laraba ake gane ta.” A yayin da yake gabatar da jawabi a bikin rufe gasar, a babban filin wasa na kasar Sin, Parsons ya bayyana cewa, gasar Beijing 2022 ta kafa wani sabon tarihi a gasar Olympic ajin kasassu ta lokacin sanyi.

Shugaban na IPC ya ce, “Abin burgewa ne yadda aka shirya gasar, filayen wasa masu kayatarwa, da wasanni masu cike da tarihi, duk wadannan an samu a lokacin muhimmiyar gasar ta Beijing. Tabbas ne, kasar Sin ta samar da abin koyi ga daukacin tsarin gasar wasannin Olympic ajin nakasassu ta lokacin hunturu wadanda zasu gudana a nan gaba. Hakika, a yanzu kasar Sin ta zama jigon wasannin Olympic ajin nakassu ta lokacin sanyi.”

Hakika bisa la’akari da irin namijin kokarin da kasar Sin ta yi, ta fuskar tsare-tsaren karbar bakuncin gasar, da yadda aka tsara filayen wasan, da kuma irin tsauraran matakan da kasar ta dauka na kandagarkin annobar COVID-19 tun gabanin gasar, da lokacin gasar, har zuwa kammala gasar, lallai zamu iya cewa, kasar Sin ta zama, zakaran gwajin dafi.(Ahmad Fagam)