logo

HAUSA

Akalla mutane 10 sun mutu a wani harin a Burkina Faso

2022-03-14 10:58:44 CRI

Mutane akalla 10 sun mutu a wani hari da aka kai mahakar zinare, ranar Asabar a yankin Sahel na kasar Burkina Faso.

Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa, kimanin ‘yan bindiga 20 ne suka farwa mahakar zinaren dake Baliata na kasar, lamarin da ya kai ga kisan mahaka 10 tare da raunata wasu da dama.

An kuma kashe wasu mutane 14 a wani hari makamancin wannan, a mahakar zinare dake yankin Seytenga a Alhamis da ta gabata.

Tun daga shekarar 2015 lamarin tsaro a Burkina Faso ya tabarbare, inda ‘yan ta’adda suka kashe sama da mutane 1,000 tare da raba wasu sama da miliyan guda da matsugunansu, a kasar dake yammacin Afrika. (Fa’iza Mustapha)