logo

HAUSA

Kasar Sin na ba da taimako ga jama’ar kasar a fannin samun guraben aikin yi

2022-03-14 19:25:00 CRI

A ganin Sinawa, shan aiki ya fi zaman kashe wando. A titunan biranen kasar, ana iya ganin yadda motoci da mutane ke wucewa cikin sauri. Kuma da wuya ne a ga wani matashi yana zama a gefen hanya ba tare da gudanar da wani aiki ba. Wannan ya nuna wani yanayin da kasar ke ciki: mutanen kasar na son aiki, kana hukumar kasar ta samar musu da isassun damammaki.

Cikin rahoton ayyukan gwamnati da kasar Sin ta gabatar a kwanan baya, ta sanya burin samar da karin guraben aiki fiye da miliyan 11, da kare jimillar yawan rashin aikin yi a kasa da kashi 5.5% a bana. To ko ta yaya kasar za ta cimma wannan buri?

Da farko dai, za ta ba da taimako ga kamfanoni masu zaman kansu don su bunkasa yadda ya kamata, ta yadda za su iya samar da guraben aikin yi. A nan kasar Sin, akwai matsakaita da kananan kamfanoni miliyan 140, wadanda ke samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai kashi 85% a kasar. Sai dai wadannan kamfanoni sun fi jin radadin mummunan tasirin da annobar COVID-19 da lalacewar tattalin arzikin duniya ke haifarwa. Saboda haka gwamnatin kasar Sin ta dauki niyyar rage musu haraji da kudin da za su biya, wadanda yawan su zai kai kimanin dala biliyan 393.5, da samar wa kamfanonin karin bashi, don taimaka musu wajen jure wahalar da suke fuskantar.

Ban da haka, don samar da karin guraben ayyukan yi, ya kamata a hada karfin bangarori daban daban na al’umma. Misali, a birnin Tianjin na kasar Sin, ana samun cibiyoyin taimakawa dalibai samun aikin yi a cikin jami’o’i daban daban, wadanda su kan gayyaci kamfanoni zuwa daukar sabbin ma’aikata a cikin jami’o’in. Kana idan wani dalibi bai samu gurbin aikin yi ba a lokacin da ya kammala karatunsa, to, gwamnati za ta ba shi taimako, inda za ta ba shi damar halartar kwas na koyon sanin makamar aiki a wasu kamfanoni. Cikin wa’adin kwas din, dalibin na samun tallafin kudi daga gwamnati a kai a kai. Sa’an nan bayan da aka kammala kwas, kamfanin da ya dauki dalibin a matsayin sabon ma’aikacinsa shi ma zai samu lada. Ban da haka kuma, su hukumomi na matakin ungwanni suna ba da taimako ga nakasassu, da magidantan da babu mutane masu aiki, don su samu aikin yi, da damar fid da kansu daga kangin talauci.

Sa’an nan don raya bangaren samar da guraben aikin yi, dole ne a gudanar da aikin horaswa da kyau. Domin a wasu wuraren dake fama da koma bayan tattalin arziki, mutane su kan gamu da matsala yayin da suke neman ayyukan yi ne sakamakon rashin sanin fasahohi na wasu ayyuka. Don daidaita wannan matsala, kasar Sin za ta ware kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 15.7 a bana, don baiwa mutanen kasar damar shiga kwas, inda za su koyi wata fasahar aiki ta musamman, ko kuma inganta fasahohinsu.

Ci gaban bangare mai alaka da yanar gizo ta Internet, shi ma ya samar wa Sinawa da wasu sabbin guraben aikin yi, irinsu masu gabatar da shirye-shiryen bidiyo da masu sayar da kayayyaki a shafukan yanar gizo, da dai sauransu. Don tabbatar da hakki da moriyar wadannan mutane, kasar Sin ta dauki niyyar daidaita manufofi, don samar musu da hidimomin inshora, ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu hankali a kwance.

A cewar firaministan kasar Sin Li Keqiang, “samar da guraben aikin yi ba kawai yake shafar zaman rayuwar jama’a, har ma da aikin raya kasa”. Bayan da wani mutum ya samu aikin yi, to, zai samu kudin shiga, gami da damar samar da kayayyaki da hidimomi ga al’umma. Kana yadda ake samun kudin shiga, zai taimakawa tabbatar da kwanciyar hankali, da raya bangaren sayayya, da janyo jari, wadanda za su tabbatar da ci gaban tattalin arzikin wata kasa. Za mu iya takaita maganar zuwa: Daidaita batun samun kudin cin abinci na jama’a, tamkar daidaita maganar samun ci gaban kasa ne. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ke matukar kokarin samar da guraben aikin yi ga al’ummarta. (Bello Wang)