logo

HAUSA

MDD ta bukaci a dauki matakan magance rikicin Sudan da farfado da zaman lafiyar yankin Darfur

2022-03-13 16:41:53 CRI

Ofishin ayyukan MDD dake kasar Sudan, ya bukaci hukumomin kasar Sudan da su yi aiki tukuru domin dakile tashe-tashen hankula a dukkan sassan kasar, kana su yi kokarin maido da zaman lafiyar yankin Darfur na kasar.

Shirin MDD dake tallafawa Sudan wato (UNITAMS), ya bayyana damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula na baya bayan nan a yankin Darfur, wanda ya yi sanadiyyar hasarar gomman rayukan fararen hula, da mutuwar masu zanga-zanga biyu a babban birnin kasar Khartoum.

Tun da farko, kafafen yada labaran cikin gidan kasar, sun bayyana cewa, fadan kabilanci da ya barke a ranar Alhamis a yankin Jebel Moon a jahar Darfur ta yammacin kasar Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17.

Sanarwar da hukumar mai zaman kanta ta fitar tace, an kashe mutane biyu cikin masu zanga-zangar a Khartoum a ranar Alhamis.

Sudan tana kara fuskantar matsalolin ricikin siyasa ne, tun bayan da babban kwamandan sojan kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ya ayyana kafa dokar ta-baci a kasar a ranar 25 ga watan Oktoban 2021, kana ya kuma rusa majalisar mulki da gwamnatin kasar.

Tun daga wancan lokacin, birnin Khartoum da sauran biranen kasar suke kara fuskantar zanga-zangar neman maido mulkin farar hula a kasar.(Ahmad)