logo

HAUSA

Dalilin da ya sa gwamnatin Sin ta samu goyon baya daga al’ummun kasar

2022-03-12 16:39:34 CRI

Kamar yadda aka saba a karshen manyan taruka biyu na kasar Sin, firayin ministan kasar Li Keqiang, ya sanar da wasu sabbin matakan da gwamnatin kasar za ta dauka domin kyautata rayuwar al’ummun kasar, wadanda ake kira da “babbar tsaraba ta taruka biyu”.

Firaministan ya sanar da matakan ne a jiya Juma’a, yayin taron ganawa da manema labarai da aka kira bayan kammala tarukan.

Daga cikin matakan, akwai samar da guraben aikin yi, wanda ke da muhimmanci sosai ga rayuwar al’ummun kasa. Idan ana son kyautata rayuwarsu, akwai bukatar goyon bayan kamfanonin da aka kafa, musamman ma kananan kamfanoni da ‘yan kasuwa masu zaman kansu, saboda adadinsu na da yawan gaske a kasar. Kuma suke samar da yawancin guraben aikin yi ga al’ummun kasar. Sakamakon kididdigar da aka samar ya nuna cewa,  a halin yanzu adadin ‘yan kasuwa masu zaman kansu a kasar Sin ya kai miliyan 100, wadanda ke samar da guraben aikin yi kusan miliyan 300 ga al’ummun kasar.

A bana, gwamnatin kasar Sin ta tabbatar da cewa, kafin karshen watan Yunin dake tafe, za ta rage harajin da kananan kamfanoni za su biya, kuma za ta dauki wasu sabbin matakai domin taimakawa sana’o’in dakin cin abinci da yawon shakatawa da jigilar fasinjoji da sauransu, ta yadda za a cimma burin kyautata rayuwar al’ummun kasar. (Jamila)