logo

HAUSA

Sabuwar masana’antar samar da Suga da Sin ta gina a Habasha, ta fara aiki

2022-03-12 17:04:35 CRI

 

Kamfanin samar da suga na kasar Habasha, ESC, ta bayyana cewa, sabuwar masana’tarta na samar da Suga ta Tana Bales No.1 sugar factory, ta fara aiki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, kamfanin ESC ya ce masana’atar sugan, wadda kamfanin gine-gine na CAMCE na kasar Sin ya gina, ta fara aikin samar da Suga a ranar Alhamis, bayan shafe watanni tana gudanar da shirye-shirye.

An fara aikin ginin masana’atar sugar dake yankin Amhara na arewacin kasar ta gabashin Afrika ne a shekarar 2012, inda aka tsara kammalawa cikin watanni 18. Sai dai, aikin ginin bai tafi kamar yadda aka tsara ba. inda zuwa karshen shekarar 2017, kaso 60 na aikin kadai aka kammala.

CAMCE, wanda mallakin kamfanin samar da injinan masana’atu na kasar Sin ne, ya karbi aikin ginin ne a watan Satumban 2019.

ESC ya bayyana cewa, ana sa ran masana’atar zata samar da suga metric ton 20,000 a kashen shekarar kudi ta kasar da ake ciki ta 2021/2022, wadda zata zo karshe a ranar 7 ga watan Yuli. (Fa’iza Mustapha)