logo

HAUSA

Asalin “Taruka biyu” shi ne al'adun dimokuradiya na kasar Sin

2022-03-11 17:19:10 CRI

Tun daga ranar 4 zuwa ta11 ga wata, an gudanar da “taruka biyu” na wannan shekara a kasar Sin, wato tarukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar, wato kamar majalisar wakilai da majalisar dattawa na Tarayyar Najeriya. 

Tarukan 2 na kasar Sin, wadanda ake gudanar da su a duk shekara, suna da ma’ana mai muhimmanci. Saboda wakilan jama’ar kasar Sin da ‘yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta al'ummar kasar suna yin amfani da wannan dama wajen gabatarwa manyan shugabannin kasar ra'ayoyi daban daban na daukacin jama’ar kasar, dangane da bukatunsu, da moriyarsu, da burikan da suka sanya gaba.

Wannan ma’ana ta musamman game da “taruka 2” na kasar Sin, ta sa jama'ar kasar Sin ke kallonsu a matsayin wani muhimmin dandali na aiwatar da tsarin dimokuradiya a kasar. Inda ake ba jama'ar kasar cikakken iko na sa ido kan harkokin mulki, da yin tasiri kan wasu muhimman ayyuka masu alaka da daidaita manufofin kasa, da tsara sabbin dokoki.