logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda sama da 120

2022-03-11 09:42:49 CRI

 

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a ranar 10 ga wata cewa, dakarunta sun kaddamar da gagarumin matakin murkushe kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a shiyyar arewacin kasar cikin makonni biyu da suka gabata, inda suka yi nasarar hallaka ‘yan bindiga akalla 121.

Kakakin rundunar sojojin Najeriyar, Bernard Onyeuko, ya fadawa kafafen yada labarai cewa a cikin makonni biyun da suka gabata, sojojin Najeriya sun kaddamar da gagarumin shirin yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na "Boko Haram" da “kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci a yammacin Afrika wato ISWAP” a shiyyar arewacin kasar. Sojojin sun yi nasarar kwace makamai masu tarin yawa da kayan yaki a lokutan kaddamar da farmakin. (Ahmad)