logo

HAUSA

Kamaru ta kaddamar da gangamin yaki da maleriya na shekara guda

2022-03-11 11:05:46 CRI

 

A jiya Alhamis, jamhuriyar Kamaru ta kaddamar da shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro wato malariya, mai taken, “kawar da malariya,” a yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da cutar a kasar.

Manaouda Malachie, ministan lafiyar kasar, ya bayyana a lokacin kaddamar da shirin a Yaounde, babban birnin kasar cewa, za a gudanar da gangamin yaki da cutar a dukkan yankunan kasar, kuma musamman shugabannin ‘yan kasuwa, da shugabannin siyasa, da sarakunan gargajiya, da malaman addinai, za su taka rawa a gangamin yaki da cutar a kasar.

Malachie, ya fadawa ‘yan jaridu cewa, wannan daya ne daga cikin shirin gangamin yaki da cutar malariya mafi girma da aka kaddamar a kasar, da nufin karfafawa jami’ai gwiwa don rage yaduwar cutar, da rage adadin mutanen da ke mutuwa a sanadiyyar cutar malariyar, da kuma kawar da mummunan tasirin da cutar ke haifarwa ga tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma.

A bisa rahoton shirin yaki da cutar malariya na kasa da kasa na shekarar 2021, Kamaru ne kasa ta 11 mafi fama da cutar a duniya.(Ahmad)