logo

HAUSA

Kasar Sin ta ciri tuta a fannin kyautata rayuwar masu bukata ta musamman

2022-03-10 16:02:09 CRI

Ko shakka babu, mutane masu bukata ta musamman dake zaune cikin al’ummun duniya, muhimmin bangare ne na jama’ar dake matukar bukatar kulawa, da lura da agaji, kasancewar su mutane da ba za su iya yin wasu abubuwa na bukatun rayuwa da kan su ba.

Lura da haka ne ya sa hukumomi a matakai daban daban, ke yin kiraye kiraye ga masu ruwa da tsaki, don gane da bukatar kara lura da bukatun masu nakasa. Bisa hakan ya sa a nan kasar Sin, mahukuntan kasar ke gudanar da manufofi daki daki, na shawo kan matsaloli da wannan rukuni na mutane ke fuskanta, musamman cikin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.

An tanadi irin wadannan manufofi, cikin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin karo na 13, wanda kasar ta aiwatarwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, inda karkashin su aka tanadi samar da karin hidimomin gyara dubban gidajen kwana ga masu bukata ta musamman, da sauran matakan kawar musu da talauci.

Kaza lika kasar Sin ta yi rawar gani, wajen aiwatar da gyare-gyare ga manyan ababen more rayuwa da wannan rukuni na al’umma ke bukata a fannin zirga-zirga, wato yayin da suke tafiye tafiye a titunan mota, da jiragen kasa, da na sama da sauran su.

A makarantu ma, an samar da na'urori na zamani dake iya taimaka musu, wajen saukakawa koyo da koyarwa. Har da ma fannin amfani da yanar gizo domin raya sana’o’i, ko saye da sayarwa, da ma samun nishadi. Kaza lika suna samun hidimomi na kula da tsofaffi masu bukata ta musamman, baya ga fannin wasanni, wanda a shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke kara samun tagomashi a bangaren raya wasannin ajin masu bukatar musamman.

Bisa wadannan dalilai da ma wasu, muna iya ganin yadda gwamnatin kasar Sin ta yi namijin kokari, wajen kara inganta rayuwar masu bukatar musamman, ta yadda za su samu damar yin kyakkyawar rayuwa, kamar dai yadda burin mahukuntan kasar yake, cewa ba za a bar kowa a baya ba, yayin da ake aiwatar da muhimman manufofin kyautata rayuwar al’umma. (Saminu Alhassan)