logo

HAUSA

Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza cigaban wasannin ƙankara na Sin

2022-03-10 15:38:19 CRI

Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza cigaban wasannin ƙankara na Sin

A ranar 4 ga wata, an ƙaddamar da gasar Olympics ta lokacin sanyi da kuma taro karo na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin ta 13 a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar, wasu mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar waɗanda ke halartar taron sun bayyana cewa, Beijing ne birni na farko a faɗin duniya, wanda ya shirya gasar Olympics na lokacin zafi da na lokacin sanyi, don haka an gina wasu filayen wasa da ɗakunan wasa da dama a birnin, duk waɗannan za su taka rawa kan dauwamammen cigaban duniya.

A bayyane an lura cewa, birnin Beijing ya samu manyan sauye-sauye tsakanin shekarar 2008 zuwa 2022, haka kuma an samu saurin ci gaban ƙasar Sin cikin waɗannan shekarun da suka gabata, to game da yadda ake amfani da filayen wasannin Olympics bayan da aka kammala gasar?

Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar kuma mataimakin shugaban sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing Shen Jin ya yi tsokaci cewa, gina filayen wasa bisa ma’aunin gasar Olympics, tare kuma da yin la’akari kan yadda za a sake yin amfani da su bayan kammala gasar, aiki ne mafi muhimmanci da sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ya yi, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fasalin filayen wasa, an fi mai da hankali kan batun yadda za a gyara ko kuma sake yin amfani da su a nan gaba.

Yadda hada-hadar cinikin ’yan wasa ke kasancewa

Ƙungiyar Paris Saint-Germain ta shirya tsaf, don bai wa ɗan wasan ƙungiyar mai shekara 23 Kylian Mbappe sabon kwantiragi kan albashi mai ɗimbin yawa na Yuro 799,000 a duk mako, domin ya zauna, inda ita kuma Real Madrid ta ce, tana son sayen ɗan wasan na Faransa.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti, mai shekara 62, ya bayar da mamaki bayan ya shiga cikin jerin waɗanda ake sa ran za a zaɓa, domin zama kocin Manchester United na gaba.

Bayern Munich da Tottenham da Arsenal suna son sayen ɗan wasan bayan Middlesbrough xan ƙasar Ingila mai shekara 21, Djed Spencer, wanda a halin yanzu ya tafi aro Nottingham Forest.

Tsohon ɗan wasan tsakiyar Everton da Colombia, James Rodriguez, mai shekara 30, ya sa ƙungiyarsa ta Everton ta zama cikin shiri bayan ya nuna alamun yiwuwar komawarsa daga Qatar.

Barcelona na sa ran shawo kan ’yan wasan bayan Chelsea da Denmark, wato Andreas Christensen, mai shekara 25 da kuma Cesar Azpilicueta na ƙasar Sifaniya, domin su koma ƙungiyar kyauta a ƙarshen wannan kakar.

Buhari Ya Gwangwaje ‘Yan Kwallon Kafa Da Gidajen Zama

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika alkawarin shekaru 28, kan yadda ta amince da rabon gidaje ga Tawagar Super Eagles 22 na shekarar 1994 a jihohinsu da suka fito.

 Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a garin Lafia, jihar Nasarawa,

 Litinin, 7 ga Maris, 2022, a lokacin kaddamar da kammala gidaje a karkashin shirin gwamnatin na samar da gidaje.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin karamin ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Muhammed Abdullahi, ya bayyana kammala ayyukan gidaje a matsayin cika alkawarin kawo sauyi da gwamnatinsa ta yi wa al’uma.