logo

HAUSA

Lokaci ya yi da Turai za ta fice daga tarkon Amurka!

2022-03-10 19:19:39 CRI

A jiya Laraba bisa agogon Amurka, majalissar wakilan kasar ta kada kuri’u, na hana shigar da danyen mai, da iskar gas da kwal na kasar Rasha cikin Amurka. Ya zuwa yanzu, wannan shi ne mataki mafi tsauri da Amurka ta dauka cikin jerin takunkumai kan Rasha. To sai dai kuma, al’ummun nahiyar Turai na kallon matakin a matsayin takunkumi kan Turai maimakon Rasha!

Ko shakka babu, ra’ayin na su na kan turba. Tun bayan barkewar rikicin Rasha da Ukraine, ba tare da la’akari da tarihin matsalolin Ukraine ba, da irin tasirin da kara matsawar NATO zuwa gabashi zai haifar, Amurka ta yi hadin gwiwa da kawayen ta na Turai, wajen kakabawa Rasha takunkumai. Sai dai kuma rashin lura da illar takunkuman, ya sa kasashen Turai tsintar kan su cikin mummunan tasirin tashin hankalin dake gudana. (Saminu)