logo

HAUSA

Gaggauta goge bayanan dakin gwaje gwaje ko me Amurka ke tsoro?

2022-03-09 20:56:05 CRI

 

Ma’aikatar tsaron Rasha, ta ce a baya bayan nan ta gano bayanai game da wani shirin binciken kwayoyin halittu na ayyukan soji, wanda kasar Amurka ke samar da kudaden gudanarwa a kasar Ukraine, yayin da dakarun Rashan ke kutsawa Ukraine din. To sai dai kuma ya zuwa karshen wata Fabarairun da ya gabata, ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, ya gaggauta goge dukkanin bayanai masu nasaba da dakin binciken na Amurka daga kan shafin sa na yanar gizo. Ko shakka babu wannan rufa rufa ta sanya tambayar ko me Amurka ke tsoro? Cikin daruruwan dakunan gwaje gwajen kwayoyin halittu da Amurka ke da su a kasashen duniya daban daban ciki har da Ukraine, shin ko me Amurka ke boyewa?    (Saminu)