logo

HAUSA

Kasashen Habasha da Djibouti sun kulla hadin gwiwa don raya aikin sufurin jiragen sama da na ruwa a tsakanin Sin da Afirka

2022-03-09 09:57:44 CRI

 

Rahotanni na cewa, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Habasha (ET) ya sanar da yin hadin gwiwa da Air Djibouti da rukunin masanaantun kasar ta Djibouti (IDIPO), domin fara zirga-zirgar jiragen sama da na teku.

Wata sanarwa da kamfanin na ET ya fitar, ta bayyana cewa, yarjejeniyar za ta mayar da hankali ne wajen yin jigilar kayayyaki daga yankunan kasar Sin zuwa yankin ciniki cikin 'yanci na Djibouti ta teku, daga nan kuma a dauki kayayyaki ta jirgin sama daga filin jirgin saman kasa da kasa na Djibouti.

Kamfanin jiragen sama na Habasha ya kara bayyana cewa, hadin gwiwar wadda za ta rage lokaci da makamashi da ake amfani da su wajen jigilar kayayyakin, za kuma ta habaka kasuwar kayayyaki a Afirka.

A cewar kamfanin na ET, yarjejeniyar sufurin, za ta baiwa 'yan kasuwa damar yin odar kayayyakinsu daga kasar Sin zuwa Afirka, ta tashar jiragen ruwa na Djibouti, kuma ET na saukaka zirga-zirgar jiragen sama zuwa sassa daban-daban na Afirka ta hanyar babbar hanyar zirgar-zirgarsa.

Kayayyakin da za a rika jigilar su dai, sun kunshi na'urorin laturoni da na amfani gida.(Ibrahim)