logo

HAUSA

Sin na goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

2022-03-09 19:41:31 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta kafar bidiyo, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a jiya Talata, inda ya shaida musu cewa, Sin tana matukar damuwa game da barkewar yaki a Turai, tana kuma goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ta yadda za a kai ga haye wahalhalu, da cimma sakamako mai amfani. Kaza lika shugaban na Sin ya ce yana goyon bayan kasashen Faransa da Jamus, a fannin samar da daidaito, da tsari mai inganci na wanzar da tsaron Turai, bisa moriyar nahiyar.

Wannan ganawar kari ce kan wadda ta gabata, tun bayan da Faransa ta karbi jagorancin karba karba na kungiyar tarayyar Turai ta EU, da kuma kama aikin sabon shugaban gwamnatin Jamus Mr. Olaf Scholz.

Sassan 3 sun maida hankali ga tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yanayi da ake ciki a Ukraine, inda kalaman shugaba Xi suka sake shaida cewa, har kullum Sin na goyon bayan adalci, game da rikicin dake faruwa, tana kuma bin matakai bisa tsari, da sanin ya kamata, da kare martabar ta a matsayin ta na babbar kasa.    (Saminu)