logo

HAUSA

Zama Lafiya Ya fi Zama Dan Sarki

2022-03-09 20:04:24 CRI

Kasa ta kan amsa sunanta ne a duniya, ko dai saboda ci gaban da ta samu a fannin tattalin arziki, ko kasuwanci, ko bincike a fannin sararin samaniya ko, fasahar kere-kere da sauran fannoni. Amma duk da irin wannan ci gaba da kasa ta samu, idan har babu zaman lafiya, tamkar ci gaba ne irin na mai hakar rijiya.

Kasashe irinsu Amurka dake daukar kanta a matsayin ‘yar sandar duniya, ta kan bugi kirgi a wasu lokuta ta rika ayyana kanta a matsayin kasar da babu kamar ta a dukkan fannoni a duniya. Sai dai ga mai bibiyar kafofin watsa labarai, ya san irin manyan kalubalolin da take fuskanta na yawan masu fama da annobar COVID-19 da wadanda ke shekawa barzahu sanadiyyar cutar. Ga kuma uwa uba rashin kwanciyar hankali, sakamakon matsalar nuna wariyar launin fata da harbe-harben bindiga da su ma ke haddasa hasarar rayukan jama’a da ba su san hawa ba balle sauka.

Sabanin kasar Amurka, wani rahoton aiki da kotun kolin jama'a ta kasar Sin (SPC) ta fitar, na nuna cewa, kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fi zaman lafiya a duniya, baya ga kasancewarta kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya da kuma ci gaban da ta samu a fannin kirkire-kirkire na zamani, Rahoton wanda aka mika wa majalisar wakilan jama’ar kasar Sin domin tattaunawa, ya bayyana cewa, adadin manyan laifuffuka iri-iri guda takwas, kamar kisan kai, da fyade da kuma satar mutane, ya ragu matuka, yayin da yawan irin wadannan laifuffuka shi ma ya ragu sosai.

Jagororin kasar Sin sun sha bayyana muradun kasar a wuraren taruka daban-daban, na ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ta hanyar mutunta juna da tattaunawa da daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari maimakon yin fito-na-fito. Na baya-bayan nan shi ne, irin shawarwarin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar kan yadda za a daidaita duk wani rashin zaman lafiyar dake faruwa a sassan duniya, yayin taron manema labarai da aka kira a gyefen manyan tarukan kasar biyu dake gudana yanzu haka, wato taron majalisar wakilan kasar(NPC) da na majilisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar(CPPCC), ta yadda za a samu duniya mai zaman lafiya da wadata da kowa zai ji dadin zama a cikinta. Domin zama lafiya, aka ce ya fi zama dan sarki (Ibrahim Yaya)