logo

HAUSA

Taruka 2 na kasar Sin na kunshe da abubuwa masu tarin yawa da tasiri irin na dimokaradiyya

2022-03-08 19:19:32 CRI

Manyan taruka 2 na siyasar kasar Sin, na kunshe da muhimman tagogi, wadanda ta cikin su duniya ke iya kara fahimtar ingancin dimokaradiyyar kasar.

Yayin tarukan na bana, wakilan jama’a kimanin 5,000, da mambobin majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa, sun taru a birnin Beijing, domin tattauna al’amuran da suka shafi kasa, ta yadda za a hade tunanin al’umma da burikan su zuwa manyan manufofin bunkasa kasa.

Ko kasa na bin salon dimokaradiyya ko a’a, muhimmin abu shi ne al’ummar ta su zama suna iya jagorantar kasar su. Manufar nan ta "dimokaradiyyar al’umma dake gudana ta dukkanin sassa " wadda JKS ta gabatar, na shafar dukkanin bangarorin jagorancin kasa, ta kuma hade dukkanin fannonin dimokaradiyyar kasar Sin, wadda ke baiwa ‘yan kasa damar mulkar kasar su.  (Saminu)