logo

HAUSA

Kasashen Afrika sun yi kira da a hada hannu wajen karfafa dabarun samun ci gaba mai dorewa

2022-03-08 10:04:11 CRI

 

Kasashen Afrika sun jaddada bukatar hada hannu wajen karfafa dabarun samun ci gaba mai dorewa da farfadowa daga tasirin annobar COVID-19, domin tabbatar da dukkansu sun shawo kan tasirinta.

Wannan na zuwa ne bayan kammala taron nahiyar karo na 8 kan muradun ci gaba mai dorewa, inda kuma aka amince da yarjejeniyar Kigali kan kyawawan akidu da mafitar da za ta inganta aiwatar da burikan ci gaba mai dorewa a Afrika.

Yarjejeniyar ta Kigali, ta yi kira ga kasashen Afrika su yi amfani da sabbin hanyoyi da kirkirar mafita da fasahohi, ciki har da inganta hadin gwiwa da bangarori masu zaman kansu da makarantu da kungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, wajen gina tsarin kididdiga na kasa mai karfi da juriya, kuma mai dorewa.

Manufar taron, wanda hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (UNECA) da gwamnatin Rwanda da hadin gwiwar hukumar kula da tarayyar Afrika da bankin raya nahiyar Afrika da sauran wasu hukumomin MDD suka shirya, ita ce nazari da karfafa matakan cimma muradun ci gaba mai dorewa na MDD zuwa shekarar 2030 da ajandar ci gaba ta nahiyar ta shekaru 50, wato zuwa shekarar 2063.

Kasashen Niger da Cote d’Ivoire, sun bayyana sha’awarsu ta karbar bakuncin taron na gaba, wanda zai gudana a yankin yammacin Afrika a watan Maris na 2023, inda ofshin kula da taron zai yanke shawara.  (Fa’iza Mustapha)