logo

HAUSA

Mata iyayen al’umma

2022-03-08 16:56:05 CRI

Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da muhimmancin mata ga al’umma da fadakarwa game da wariyar da ake nuna musu. Muhimmancin mata a cikin al’umma abu ne da ba zai taba misaltuwa ba, domin su ne tubali, kuma ginshikin al’umma ta gari, kasancewarsu malamai na farko ga ‘ya’yansu. Shi ya sa ake cewa, ilmantar da mace daya tamkar ilmantar da al’umma ne.

A yanzu ana samun karin mata dake neman ilimi da tafiyar da sana’o’i da shiga ayyuka masu sarkakiya da a baya maza ne kadai aka sani da yin su, inda suke samun nasarori na ban mamaki. Sai dai duk da irin wannan kokari da suke yi, ana ci gaba da nuna musu wariya da tauye musu hakki, tare da raina kwarewarsu.

A wannan rana dake zaman wata kafa ta tunatarwa ga shugabanni da al’umma game da matsalolin da mata suke fuskanta, ya kamata a ce an kara nazari domin samar da kyakkyawan kudurin shugabanci da albarkatu, har ma da dokoki.

A kuma wannan gaba ne zan jinjinawa kokarin kasar Sin a wannan fanni, ganin yadda a jiya, majalisar wakilan jama’ar kasar dake zamanta na shekara, ta gabatar da kudurin ba mata karin kujeru a majalisar da a yanzu mata suke da kaso 25 cikin dari na mambobinta. A kowacce majalisar wakilan Sin, akan samu karin adadin mata masu wakilci, inda a majalisar ta 13 ta yanzu, ake da mata 742. A ganina, wannan babban albishir ne ga matan kasar Sin, domin ya nuna cewa, kasar na maraba da gudunmuwarsu, kuma ta san muhimmancin da suke da shi ga ci gabanta da al’ummarta. Don haka, wannan kamar kira ne ko zaburarwa ga sauran kasashe masu tasowa dake ganin babu abun da mata za su iya tabukawa ga harkokin shugabanci, ko kuma suke daukar matan a matsayin kalubale. Wannan ya zama misali a wajensu, idan suka yi la’akari da irin ci gaban da kasar Sin ta samu, wanda zai nuna musu cewa, ba mata dama da ba su kariya, ba zai taba zama koma baya a gare su ba, sai ma dai hanyar samun karin ci gaba. (Fa'iza Muhammad Mustapha)