logo

HAUSA

Sheriff Ghali Ibrahim: Kasa da kasa za su ci gaba da cin gajiya daga damammakin ci gaban kasar Sin

2022-03-08 13:59:15 CRI

Kwanan nan ne aka bude taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC a takaice, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda firaministan kasar Li Keqiang, ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati na bana, a madadin majalisar gudanarwar kasar.

Cikin rahoton, firaminista Li ya waiwayi muhimman nasarorin da kasar Sin ta samu a shekarar da ta gabata, da hasashen abubuwan da kasar za ta yi a wannan shekarar da muke ciki wato 2022. 

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, kana masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, ya yi tsokaci kan wannan muhimmin rahoto, inda kuma ya bayyana ra’ayinsa kan yadda kasa da kasa, musamman kasashen Afirka za su iya amfana daga ci gaban kasar Sin. (Murtala Zhang)