logo

HAUSA

Amsoshin Da Wang Yi Ya Bayar Sun Bayyana Yadda Kasar Sin Ke Daukar Nauyin Dake Wuyanta

2022-03-08 11:51:50 CRI

BY CRI HAUSA

Yayin taron manema labarai da aka yi a jiya Litinin kan manyan taruka 2 na kasar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya amsa tambayoyi 27 da aka gabatar masa a cikin kusan sa’o’i 2, inda ya bayyana matsayin da Sin take dauka kan wasu batutuwan duniya, ciki har da yanayin da Ukraine ke ciki da huldar kasa da kasa da gudanar da harkokin duniya da sauransu.

Kasar Sin ta gabatar da shawarwarinta guda 4 bisa gaskiyar halin da ake ciki kan batun Ukraine, tare da yin kira ga kasashen duniya da su mai da hankali kan sulhuntawa tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki da magance matsalar jin kai. Kuma ta gabatar da shawarwari guda 5 game da wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da share fagen taro karo na 3 na ministocin harkokin wajen kasashen dake makwabtaka da Afghanistan.

Game da batun tinkarar cutar COVID-19 da sauyin yanayi da sauran kalubalen duniya, Wang Yi ya yi tsokaci cewa, Sin ta yi ta samar da gudummawarta ga kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa, don hada kan kowa da kowa wajen tinkarar barazana tare.

Ya ce, Sin ba ta canja matsayinta na shimfida zaman lafiya da raya duniya da kiyaye zaman oda da doka a duniya ba. Bugu da kari, ya ce Sin kasa ce mai sauke nauyin dake wuyanta, kuma za ta ci gaba da nacewa ga manufofin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, don hadin kanta da kasashen duniya da nufin cin gajiya tare nan gaba. (Amina Xu)