Wang Ting: Kokarin samarwa mazauna kauyen Xuejia tsayayyen kudin shiga ta hanyar samun ci gaba ba tare da bata muhalli ba
2022-03-07 13:53:31 CRI
A lokacin da nake hira da Wang Ting ‘yan watannin da suka gabata, ta dan dakata ta nunawa ‘yarta hoton wata gonar ganyen shayi. Ko meye dalili? Gonar ganyen shayin na da mazauni ne a Xuejia, wani kauye dake gundumar Shimen ta lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Bayan ta kalli hotunan, diyarta ta jinjina mata, tana mai cewa, “mama, ke gwarzuwa ce! Kin yi gadon gurguzanci.” Wang Ting ta murmusa, ta fada min cewa, “duk da cewa wasu iyaye ba sa iya zama tare da ’ya’yansu a lokacin da suke tasowa, wadannan iyaye na tasiri kan ‘ya’yansu. A don haka, suna taimakawa ’ya’yansu yayin da suke girma.” A hakika, wannan wani darasi ne da Wang Ting ta koya daga mahaifinta, Wang Xinfa.
Wang Ting da Wang Xinfa, dukkansu sun taba samun lambar yabo ta nagarta a yakin da kasar Sin ke yi da talauci. A watan Fabrairu, Wang Ting ta halarci wani taron karramawa a Beijing, kuma bayan ta karbi lambar yabo, ta koma kauyen Xuejia da jan furen da ta sanya yayin bikin. Ta ajiye wannan fure a kabarin mahaifinta da ya mutu a shekarar 2017. Wang Ting ta ce, “Baba, na ba ka kyautar wannan fure. Lambar yabo da muka samu, taka ce da kuma ta kauyen Xuejia.”
Wang Ting ta tashi daga Beijing zuwa kauyen Xuejia a karon farko ne a lokacin bazara na shekarar 2015, domin ziyartar mahaifinta. Wang Xinfa, wanda ya shiga rundunar sojin kasar Sin a shekarar 1969, ya koma birnin Shijiazhuang dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin saboda aiki a shekarar 1982, bayan ya yi ritaya daga aikin soji. Wang Xinfa na da wani buri, wato karfafawa sojojin da suka yi ritaya gwiwar yunkurawa domin taimakawa al’umma.
A shekarar 2013, Wang Xinfa ya amsa kiran JKS na shiga aikin yaki da talauci. Ya kaura daga Shijiazhuang zuwa gundumar Shimen domin taimakawa mazauna kauyen Xuejia fita daga kangin talauci.
Dutsen Liuta na da mazauni a tsakiyar kauyen Xuejia. Sojojin kasar Sin 68 ne suka mutu a kan dutsen yayin da suke fadan ‘yantar da kasar yayin juyin juya hali. Mazauna kauyen Xuejia ne suka binne su. Wannan tarihi ya taba zuciyar Wang Xinfa, don haka ya yanke shawarar gina makabarta ga sojojin. “Mahaifina ya ziyarci gidajen mutanen kauyen Xuejia daya bayan daya, domin karfafa musu gwiwar taimakawa wajen gina makabarta ga sojojin 68. Ya tattaro mata daga kauyen domin su saka tutoci 68 ga sojojin. Ta hanyar sake binne sojojin a sabuwar makabarta da aka sanya mata suna “Shan He Yuan,” a kan dutsen Liuta, babana ya ce yana fatan mazauna kauyen ba za su taba mantawa da tarihi ba, haka kuma za su dora kan turbar da sojojin ‘yantar da kasar suka samar”, cewar Wang Ting.
A ranar 23 ga watan Fabrairun 2017, Wang Xinfa ya mutu saboda gajiya, sakamakon aiki fiye da kima. Wang Ting na iya tuna yadda mazauna kauyen suka yi jimamin mutuwarsa. Ta ce, “Mazaunan, cikinsu har da manya da kanana, sun durkusa suna kallo, yayin da aka binne mahaifina a Dutsen Liuta. Wadanda suka fita ci rani da dama ma, sun je sun ga kabarin mahaifina, a lokacin da suka dawo kauyen Xuejia”. Domin ci gaba da aikin mahaifinta na taimakawa mutanen kauyen yaki da talauci, Wang Ting ta bar aikin da take yi a Beijing, ta koma kauyen Xuejia domin taimaka musu.
Kafin ya mutu, Wang Xinfa ya rubuta wani tsarin raya kauyen Xuejia. Yana son inganta tarihin juyin juya hali da raya kauyen ta hanyar da ba za ta gurbata muhalli ba.
Wang Ting ta ce ta yi mamaki a lokacin da ta isa kauyen Xuejia karo na farko a shekarar 2015. “Na taso ne a arewacin kasar Sin. Na saba da rayuwa a shimfidadden wuri. Kauyen Xuejia na kan tsauni. Wurin cike yake da duwatsu, bai dace da noma ba”, cewar Wang Ting. Wannan ne dalilin da ya sa mazaunan suka zabi noman ganyen shayi, wanda zai iya dacewa da yanayin tsaunika, domin samun kudin shiga.
A shekarar 2014, Wang Xinfa ya gabatar da shawarar noman ganyen shayi ba tare da amfani da sinadaran zamani ba. “Babu amfani da maganin kwari da sinadaran taki, kuma ganyen shayi masu kyau kadai za a rikawa tsinkowa. Da farko, mazaunan ba su amince da wadannan sharuda masu tsauri ba”, cewar Wang Ting. Wang Xinfa ya fitar da kudi daga aljihunsa domin noman ganyen shayin ba tare da amfani da sinadaran zamani ba. Ya nuna misali ga sauran mutanen kauyen, inda ya tabbatar da cewa noman ganyen shayi ba tare da sinadaran zamani ba, zai iya samar da kudin shiga.
Bayan mutuwar mahaifinta, mutanen kauyen da dama ne suka kira Wang Ting a waya, inda suka bukaci ta taimaka ta sayar musu da ganyen shayinsu. “Babana ya mutu jim kadan bayan mutanen sun fara noman ganyen shayi ba tare da sinadarai ba. A lokacin, suna bukatar taimako”, cewar Wang Ting. Ta ziyarci kwararru a lardin Hunan, wadanda ke da gogewa kan noma da sarrafawa da sayar da ganyen shayi. Ba da jimawa ba ta gano cewa, mazauna kauyen na bukatar wani tsari na bai daya na inganta noma da tsinkar ganyen shayi da kuma dabarun sarrafa shi. Daga nan sai ta yi rajistar kamfanin ganyen shayi a gundumar Shimen, inda ta taimaka wajen yi wa ganyen shayin Xuejia tambari.
Kusan karshen shekarar 2020, aka kafa wata cibiyar sarrafa ganyen shayi da girmanta ya kai murabba’in mita 7330 a kauyen Xuejia. Cibiyar ta fara aiki ne a lokacin bazarar bara, bayan an yi girbin ganyen shayi. A yanzu, gonakin ganyen shayi a Xuejia, da suka mamaye fili mai kadada 106.67, sun zama alama ta raya muhalli dake samarwa mazauna tsayayyen kudin shiga.
Mazauna kauyen Xuejia na son kiran Wang Xinfa da sunan “shugaban kauye na alfarma” domin giramamawa da kuma yaba masa. Wang Ting ta yi gadon kwazon mahaifinta, inda ta ci gaba da bayar da gudunmmuwa ga ci gaban Xuejia. Cikin shekaru da dama da suka gabata, Wang Ting ta yi ta tafiya tsakanin Beijing da Hunan. Yayin lokacin hunturu na shekarar 2018, da take ziyara a Xuejia domin tantance inda za a gina cibiyar sarrafa ganyen shayi, ta kamu da rashin lafiya, daga bisani ta gano cewa tana da cikin danta na biyu. Ta tafi da jaririnta Xuejia a lokacin ko watanni 4 bai cika ba, domin ta kula da shi tare kuma da sa ido kan aikin ginin tashar sarrafa ganyen shayin.
A lokacin da Wang Xinfa yake aiki a Xuejia, ya samu goyon bayan matarsa da kuma Wang Ting. A yanzu, Wang Ting na samun goyon bayan mijinta da surikanta. Labaran yadda kakansu da mahaifiyarsu ke taimakawa mutanen kauyen yaki da talauci, ya fadada ilimin yaran Wang Ting 2, kuma ya ba su kwarin gwiwar alfahari da rayuwarsu dake cike da jin dadi.
Wang Ting ta ce, “Lambar yabo na jami’i mafi nagarta a yakin da kasar Sin ke yi da talauci, babbar girmamawa ce a gare ni da mahaifina. Ta bayyana kokarin mahaifina, kuma a gare ni, ta saita alkiblar da zan ci gaba da bi wajen aiki.” Tana fatan cimma burin mahaifinta, wato samun wadata a zuci da kuma a zahiri tare da jama’ar. “Babana na da burin ganin mun yi ammana da jam’iyyarmu da kuma kasancewa masu kishin kasa. Ya kuma yi fatan kowa a kauyen Xuejia, zai yi rayuwa mai dadi. Hakki na ne hada hannu da mutanen kauyen wajen ci gaba da lalubo hanyoyin farfado da kauyen da ci gabansa tare da kirkiro sabbin abubuwa. Ina son tamaikawa wajen gina kauyen Xuejia mai kyau da ci gaba”, cewar Wang Ting.