logo

HAUSA

Ra’ayin Dimokuradiya Yana Cikin Al’adun Gargajiyar Sin

2022-03-07 19:26:35 CRI

Sharhi daga Bello Wang

Yanzu haka ana gudanar da “Taruka 2”,wato tarukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar, a birnin Beijing. Inda mahalarta tarukan suke tattara ra’ayoyin jama’a da bukatunsu, tare da mika su ga manyan jami’an kasar. Wannan wani muhimmin bangare ne na tsarin Dimokuradiya na kasar Sin.

Da muka tabo maganar Dimokuradiya, mun san kasashe daban daban sun fi kwaikwayon tsarin Dimokuradiya na kasashen yamma. Sai dai mene ne asalin tsarin Dimokuradiya na Sin? Game da wannan tambaya, za mu iya neman amsarta daga cikin wasu tsoffin littattafan kasar Sin.

Cikin wani tsohon littafi mai suna “Li Ji”, an rubuta cewa “Duk wata kasa ta daukacin jama’arta ce”, inda aka bukaci mai mulki da ya zabi masu hazaka da kwarewa daga cikin al’umma, domin su taka rawa a harkokin mulki.

A cikin wani littafi mai suna “Shang Shu”, an bayyana cewa “Jama’a tushe ne na wata kasa”. Sa’an nan wani shehun malami na kasar Sin mai suna Mencius ya karbi wannan tunani, inda ya bayyana shi sarai kamar haka: “Jama’a sun fi daraja. Filayen kasa tana biyo baya. Yayin da sarki ba shi da muhimmanci.”

Tunanin Dimokuradiya ya kunshi ra’ayin samun zaman daidaito tsakanin mutane. An fara samun ra’ayi na zaman daidaito daga cikin tunanin shehun malami mai suna Confucius, wanda ya bayyana cewa “Duk wani abun da ba a son shi, kar a aikata shi kan sauran mutane”. Shi ma Mencius ya ce, “Ya kamata a girmama dattawa na kansa da na sauran mutane, da kula da yaransa da na sauran mutane”.

Ban da wannan kuma, a cikin wani tsohon littafi mai suna “Guo Yu”, an bayyana ra’ayi na kare ‘yancin mutum na fadin albarkacin bakinsu. Inda aka ce, “Hana jama’a yin magana, tamkar toshe hanyar kogi ne. Idan an toshe hanyar kogi, za a ji radadin ambaliyar ruwa. Idan an hana mutane magana, za a fada cikin mawuyacin hali, bayan da fushinsu ya haifar da rikici.”

Sa’an nan wani littafin da ya fi tsufa a kasar Sin mai taken “Yi Jing”, ya ayyana darajar tsarin Dimokuradiya kamar haka: “Idan mai mulki yana yin musayar ra’ayi da jama’a, za su cimma matsaya kan manufofin kasa. Amma idan mai mulki ya ki sauraron ra’ayin jama’a, to, mulkin ya zo karshensa.”

Wadannan tunani game da kare hakkin jama’a, da tabbatar da ‘yancinsu a fannin mulki, sun riga sun zama wani muhimmin bangare na al’adun kasar Sin, wanda ya kasance asali na tsarin Dimokuradiya na Sin, daidai da yadda tunanin Dimokuradiya na kasashen yamma ke samun asali a garuruwan tsohuwar Girika.

Tabbas, tunani da tsare-tsaren yammacin duniya, su ma sun yi tasiri kan tsarin Dimokuradiya na kasar Sin. Cikin shekaru fiye da dari daya da suka gabata, al’adun kasashen yamma sun kutsa kai cikin kasar Sin, bisa taimakon karfin sojan su, abun da ya tilasta wa Sinawa yin gyare-gyare kan harkokin siyasar kasa. Inda suka kifar da sarki, da shigar da tsarin “Capitalism” na jari hujja, kafin daga bisani su kaddamar da juyin-juya hali na Gurguzu, da tabbatar da tsarin Dimokuradiya irin na Gurguzu. Har zuwa yanzu, wata babbar manufar da masu mulki na kasar Sin suke dauka ita ce “Yin gyare-gyare a cikin gida”.

Ta hanyar yin nazari kan tarihi, za mu iya sanin cewa, Sinawa sun gaji al’adunsu na gargajiya masu kunshe da ra’ayi na Dimokuradiya, kana sun koyi abubuwa masu kyau na tsarin Dimokuradiya na zamani na kasashen yamma. Ban da wannan kuma, suna ta aiwatar da gyare-gyare kan tsarinsu, don ya zama mai dacewa da zamani, ta yadda suka samu wani tsarin Dimokuradiya mai salon musamman na kansu. Wannan tsarin Dimokuradiya yana da amfani sosai, saboda ya dace da yanayin da kasar ke ciki, wanda yake taka muhimmiyar rawa a fannonin ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, da samarwa al’ummar kasar alfanu. Ganin haka ya sa Sinawa ke da imani kan tsarin Dimokuradiyar su. (Bello Wang)