logo

HAUSA

Taruka Biyu Na Sin Na Da Babbar Ma’ana Ga Al’ummun Duniya

2022-03-07 19:39:31 CRI

Yayin da a karshen mako aka kaddamar da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, wato taro na 5 na majalisar wakilan jama’ar kasa NPC karo na 13, da na kwamitin hukumar bada shawara kan al’amurran siyasar kasar Sin CPPCC, dake gudana a birnin Beijing, wasu kafofin watsa labaran kasa da kasa sun bayyana tarukan a matsayin masu matukar muhimmanci ba kawai ga kasar Sin ba, har ma da alummar duniya baki daya. Kamfanin watsa labarai na kasar Kenya wato KBC yana da irin wannan ra’ayi, inda ya gabatar da wani sharhi dake nuna cewa, tarukan biyu na kasar Sin wadanda ke gudana a birnin Beijing na kasar suna jawo hankalin al’ummun kasashen duniya matuka, musamman ma batun dake shafar shawarar “ziri daya da hanya daya”, saboda shawarar tana amfanar dukkan duniya, har ma tana taka muhimmiyar rawa wajen cudanyar tattalin arzikin duniya. Sharhin ya kara cewa, kasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ce ta kasashen Afirka, wadda ke zuba jari mafi yawa a nahiyar, musamman ma cikin ’yan shekarun da suka gabata, kasashen Afirka suna cin gajiya daga jarin da kasar Sin ke zubawa a nahiyar, misali a bangarorin manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a da fannin kiwon lafiya. Don haka batutuwan da za a tattauna yayin tarukan biyu na kasar Sin suna da babbar ma’ana ga kasashen Afirka. Ban da haka, shugabannin kasashen Afirka da dama suna sa ran za su kara kyautata huldar dake tsakanin kasashensu da kasar Sin, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Bugu da kari, ita ma jaridar “Observer” ta kasar Pakistan, ta wallafa wani sharhi a ranar 4 ga wata, inda aka bayyana cewa, kasar Sin ta samu amincewa daga masu zuba jari a fadin duniya, bisa salon karuwar tattalin arzikinta na cigaba mai dorewa, yanzu haka ana gudanar da taruka biyu a kasar Sin, inda ake tabbatar da cewa, idan kasar Sin ta ci gaba da samun wadata, tabbas ne daukacin kasashen duniya za su ci gajiya daga ci gaban kasar ta Sin. Hakika, dukkan manufofin raya tattalin arziki da cigaban alumma da kasar Sin ke aiwatarwa suna taka muhimmiyar rawa ga cigaban tattalin arzikin duniya. Alal misali, a cikin rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar na baya bayan nan kan ci gaban kasar Sin a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa a shekarar 2021, rahoton yace, duk da kalubaloli da dama da ake fuskanta a ciki da wajen kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, amma kasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki da kaso 8.1 bisa 100, kana yawan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya kara babban kuzari kan tattalin arzikin duniya wanda ake fadi-tashin farfadowarsa, sannan tattalin arzikin kasar Sin yana mara wa tattalin arzikin duniya baya matuka. A shekarar 2021, gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ta kai kaso 25 cikin 100. Jimilar kudaden shigi da ficin kayayyaki ya kai kudin Sin Yuan triliyan 39.1 a kasar Sin, wanda ya karu da kaso 21.4 cikin dari bisa makamancin lokacin na shekarar 2020, don haka kasar Sin ta shafe shekaru 5 a jere tana zama ta farko a duniya a fannin cinikin kayayyaki. Hakan ya nuna cewa, kasashen duniya na bukatar kayayyaki kirar kasar Sin. Al’ummar kasar Sin na sayen kayayyaki daga sassa daban daban na duniya, abin da ke nuna karin bukatunsu. Dama dai batun bullo da dabarun kyautata yanayin tattalin arzikin kasa na daga cikin muhimman ajandojin manyan tarukan shekara-shekara na kasar Sin, don haka babu tantama duniya zata ci gaba da cin gajiyar kudurorin dake kumshe a tarukan na bana. (Ahmad Fagam)