logo

HAUSA

Kwararrun Afrika sun bukaci a rungumi tsarin noma mai jurewa sauyin yanayi don kawar da yunwa

2022-03-06 16:37:25 CRI

Masana sun bayyana cewa, za a iya cimma nasarar kawar da yunwa da karancin abinci mai gina jiki a Afrika ne kadai, idan gwamnatocin kasashen suka mayar da hankali wajen kai daukin da zai tabbatar da bunkasa tsarin noma, a yayin da ake fuskantar matsin lamba daga matsalolin sauyin yanayi.

A jawabin da suka gabatar a wani taron dandali a garin Naivasha, mai tazarar kilomita 100 dake arewa maso yammacin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, dukkan kwararrun sun amince da bukatar nahiyar ta rungumi tsarin aikin gona dake jure matsalolin sauyin yanayi, yayin da fannin noma ke fuskantar barazana sakamakon tsananin karuwar matsalar sauyin yanayi.

Kwame Ababio, babban jami’in shirin sauyin yanayi da kula da muhalli na kungiyar tarayyar Afrika AU yace, zuba jari a fannin aikin gona wanda zai iya dacewa da yanayin da ake ciki, zai iya zama wata hanya mai kullewa da zata warware matsaloli na dogon lokaci da nahiyar ke fuskanta na karancin abinci.

Yace, manufofin da ake bullowa dasu, da kuma binciken kimiyyar da aka amince dasu a nahiyar sun nuna cewa, akwai bukatar a dauki matakai da zasu jure matsalolin sauyin yanayi a fannin ayyukan gona, ta hanyar amfani da fasahohin noman rani mafiya dacewa, da yin amfani da takin gargajiya, da kuma amfani da sabbin hanyoyin sauye-sauye.

George Wamukoya, shugaban tawagar kungiyar wakilan Afrika, yace taron kolin sauyin yanayi da za a gudanar a kasar Masar a watan Nuwamba, wata muhimmiyar dama ce da nahiyar ta samu wajen gabatar da bukatun neman karin kudaden aiwatar da dabarun bunkasa ayyukan noma.(Ahmad)