logo

HAUSA

Sauyin yanayi a Afirka na haifar da tashe-tashen hankula da karuwar masu gudun hijira

2022-03-05 11:50:29 CRI

 

Babban daraktan cibiyar wayar da kai game da tasirin sauyin yanayi ta Afirka, ko “Pan-African Climate Justice Alliance” Mr. Mithika Mwenda, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Afirka, da sauran jagororin hukumomin kasa da kasa, da su kara azama wajen samar da kudaden kyautata damar al’ummun nahiyar, na jure mummunan tasirin sauyin yanayi.

Mamadou Oudrago, wani mai rajin kiyaye muhalli, dan asalin kasar Burkina Faso, ya ce tasirin sauyin yanayi a yankunan kudu da hamadar saharar Afirka, na rura wutar tashe-tashen hankula tsakanin al’ummu daban daban, da tilasawa mutane barin muhallan su, baya ga rashin dorewar tsarin siyasa da hakan ke haifarwa.

Oudrago wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, ya ce tasirin sauyin yanayi na gurgunta zaman lafiya, da ingiza rikicin manoma da makiyaya a kasashe irin su Najeriya, da Mali, da Burkina Faso, matsalar dake shafar kaso mai yawa na yankunan kudu da hamadar sahara. (Saminu)