logo

HAUSA

Tattalin Arzikin Kasar Sin Yana Taimakawa Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

2022-03-05 18:04:07 CRI


Yau Asabar ne aka kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, inda rahoton ayyukan gwamnatin da aka gabatar don a dudduba shi ya yi nuni da cewa, dole ne a kara sa muhimmanci kan samun ci gaba ba tare da tangarda ba.

Shekarar 2021 tana da muhimmiyar ma’ana ga kasar Sin. Duk da barazana da kalubaloli daban daban da ta fuskanta, kasar Sin ta ci gaba da farfado da tattalin arzikinta. Ta cimma manyan manufofinta yadda ya kamata. Jimillar tattalin arzikin kasar Sin a bara ya kai dalar Amurka triliyan 3, wanda ba a taba ganin irinsa a tarihin duniya ba.

Aiki ne mai wahala da kasar Sin ta kai ga cimma kyawawan sakamako. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin na da karfin juriya wajen raya tattalin arziki, tana daidaita barazana yadda ya kamata, kana kuma hakan na da nasaba da yadda take yaki da annobar COVID-19, da kuma sa muhimmanci kan samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa ba tare da tangarda ba.

Kasar Sin ta sanya burin daga yawan GDPn kasar da kaso 5.5 bisa dari a shekarar 2022. Ta yi tunani sosai kan halin da take ciki a gida da waje ta fuskar bunkasa tattalin arziki, kana adadin ya dace da hakikanin yanayin bunkasar tattalin arziki. Ya cancanci yadda kasar Sin take raya tattalin arziki ba tare da tangarda ba.

Da zummar cimma burinta, a bana kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje, za ta duba yiwuwar nazarin bangarorin da kasashen waje ba za su iya zuba jari ba, domin tabbatar da an ba su damarmaki kamar takwarorinsu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci, a kokarin shigar da karin jarin waje. Budaddiyar kasuwar kasar Sin za ta shigar mata karin jarin waje, kana kuma za ta samar wa kamfanonin kasa da kasa damarmaki na samun ci gaba a kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)