logo

HAUSA

Xi: A karfafa ayyukan gudanar da harkokin JKS

2022-03-04 14:04:24 CRI

“Gudanar da harkokin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin yadda ya kamata” ita ce bukatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cikin taruka biyu, wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na CPPCC da kuma majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin NPC. Bayan cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 18. Sau da dama, shugaba Xi Jinping ya jaddada kira da a karfafa aikin gina JKS, da gudanar da ayyukan jam’iyyar yadda ya kamata, domin shimfida yanayin siyasa mai kyau.

Dangane da wannan batu, ga karin bayanin da Maryam Yang ta kawo mana:

Cikin taruka biyu na shekarar 2015, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a mai da hankali wajen daidaita yanayin siyasa, da yaki da cin hanci da karbar rashawa. Ya ce,“Ya kamata a karfafa aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa, da karfafa aikin bincike kan batun, da gurfanar da dukkanin wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kuliya, domin kawar da matsalar baki daya, kuma daga tushe.”

Xi Jinping yana mai da hankali matuka kan dangantakar dake tsakanin jami’an gwamnati da ’yan kasuwa, ya sha jaddada cewa, bai kamata a nemi moriya ta hanyar amfani da albarkatun siyasa ba. Kuma, a yayin da ake gudanar da taruka biyu a shekarar 2016, ya bayyana cewa, ya kamata a kafa sabuwar hulda mai kyau, kuma mai tsabta a tsakanin jami’an gwamnati da ’yan kasuwa. Yana mai cewa, "Kafa dangantaka mai kyau yana nufin yin mu’amala da kamfanoni masu zaman kansu ba tare da boye komai ba, da kuma taimaka musu wajen warware matsaloli. Kuma kafa dangantaka mai tsabta yana nufin yaki da cin hanci da karbar rashawa. A bangaren kamfanoni masu zaman kansu kuma, ya dace su rika fadin gaskiya da kuma bin doka, yayin da suke mu’amala da jami’an gwamnati da gudanar da harkokinsu.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)