logo

HAUSA

Cutar Lassa ta kashe likitoci biyu a Najeriya

2022-03-04 09:49:43 CRI

Kungiyar likitocin Najeriya ta ce, cutar zazzabin Lassa ta yi sanadiyyar likitoci biyu a cikin kwanaki uku da suka gabata.

A jawabin da kungiyar likitocin kasar (NMA) ta fitar, ta bayyana barkewar zazzabin Lassa a kasar a matsayin karin wani hari wanda kasar ke fuskanta bayan mummunar barnar da cutar COVID-19 ta haifar.

Kungiyar ta NMA ta ce, sun damu matuka game da sauran ma’aikatan lafiyar da suka yi mu’amala da likitocin da suka mutu ba tare an sani ba. Ta kara da cewa, tana bada shawarar a killace ma’aikatan lafiyar da lamarin ya shafa, sannan a ba su kyakkyawar kulawa wajen duba lafiyar wadanda aka ga suna da wasu alamomin rashin lafiya mai tsanani.

Ita dai cutar zazzabin Lassa, galibi ana iya daukarta ne ta hanyar taba yawu, ko fitsari, ko wani abin da ya fita daga jikin wasu nau’ikan beraye yayin da suka yi mu’amala da mutane, ta hanyar abincinsu, ko ruwan sha. Sannan ana iya daukar cutar daga mutum zuwa mutum yayin da wani ya taba ruwan da ya fito daga jikin maras lafiya, duk da yake hakan bai cika faruwa sosai ba. (Ahmad Fagam)