logo

HAUSA

Manya da ba sa motsa jiki suna iya gina damtse kamar manyan 'yan wasa

2022-03-04 16:32:39 CRI

Masu bincike a jami'ar Birmingham ta kasar Birtaniya sun bayyana a cikin wani rahoto da suka fitar a kwanakin baya cewa, tsofaffin da ba su taba shiga wani shiri na motsa jiki ba, suna da damar iya gina jiki kamar kwararrun 'yan wasa masu shekaru irin nasu.

Rahoton mai taken "Ba a makara don fara motsa jiki" ya nuna cewa, hatta wadanda ba su saba motsa jiki ba, suna iya cin gajiyar shirin motsa jiki kamar daga abun nauyi don kyautata karfi.

A cikin binciken, wanda aka buga a mujallar Frontiers in Physiology, masu bincike daga makarantar wasanni da kimiyyar motsa jiki ta jami'ar irmingham, sun kwatanta damar da rukunin maza guda biyu ke da ita ta gina tsoka ko damtse.

An raba rukuni na farko a matsayin kwararrun ‘yan wasa, mutanen dake cikin shekarunsu na 70 da 80, wadanda suke motsa jiki a rayuwa, kuma har yanzu suna shiga manyan matakan wasanni.

A cikin rukuni na biyu kuwa, akwai mutane masu lafiya masu shekaru iri daya, wadanda ba su taba shiga cikin shirye-shiryen motsa jiki da aka tsara ba.

Da ma masu bincike suna ganin cewa, kwararrun 'yan wasa, za su samu damar gina jiki saboda matakan da suka dace da su na lokaci mai tsawo. A zahiri, sakamakon ya nuna cewa, rukunonin biyu suna da damar da za su iya gina jiki bisa motsa jikin da suke yi.

Jagoran masu binciken Dr. Leigh Breen ya yi nuni da cewa, bincikensu ya nuna a fili cewa, babu wani abu idan ba ka kasance mai motsa jiki na yau da kullum ba a tsawon rayuwarka, kuma har yanzu za ka iya amfana daga motsa jiki a duk lokacin da ka fara.

Tabbas tsayin daka kan motsa jiki da kasancewa cikin koshin lafiya cikin dogon lokaci, shi ne hanya mafi kyau don cimma lafiyar jiki baki daya, amma ko da an fara daga baya a rayuwa, hakan zai taimaka wajen jinkirta raunin shekaru da na tsoka.

Breen ya kara da cewa, babu tabbas game da shawarwarin lafiyar jama'a na yanzu da aka gabatar game da horo mai karfi ga tsofaffi galibi.

Breen ya ci gaba da cewa, abin da ake bukata shi ne, karin jagora na musamman kan yadda mutane za su iya inganta karfin jikin su, har ma da wajen tsarin motsa jiki ta hanyar ayyukan da ake yi a gidajensu, yayin da ya tabo ayyuka kamar aikin lambu, tafiya a kasa da matakalan gida, ko daga ledar cefane. Wadannan duk za su iya taimakawa idan har an yi su a matsayin wani bangare na tsarin motsa jiki na yau da kullum. (Ibrahim)