logo

HAUSA

Saliyo ta fara koyar da yaren Sinanci a makarantun firamare

2022-03-04 10:42:29 CRI

A jiya Alhamis, kasar Saliyo ta kaddamar da shirin fara koyar da yaren Sinanci a wasu makarantun firamaren kasar biyar, a kokarin bunkasa yaren Sinanci a kasar ta yammacin Afrika.

Shirin, wanda aka fi sani da suna, Sinanci da kadan-kadan, wanda Mariatu Kargbo, wata mata ce ’yar kasar Saliyo da ta yi aiki a kasar Sin a matsayin mai zane-zane ta bullo da shirin.

A yayin bikin kaddamar da shirin, ta ce, shirin zai taiamakawa yara ’yan makarantun firamare samun damar yin magana da yaren Sinanci mafi sauki, kuma zai ba su damar samun nasarori a cikin al’umma.

Ta ce, darasin zai baiwa yaran damar yin magana da abokansu Sinawa, kuma zai taimaka musu yayin da suka shiga fagen ilmin koyon Sinanci a cibiyoyin al’adun kasar Sin na Confucius da sauran makarantu.

Mataimakiyar ministan ilmin matakin farko da na sakandare ta kasar Saliyo, Emily Gogra, ta yabawa shirin, har ma ta bada shawarar kara shi cikin manhajar ilmin makarantun kasar. (Ahmad)