logo

HAUSA

Amurka mai ikirarin wai tana “kare hakkin bil Adam”

2022-03-04 15:22:42 CRI

Bayan harin “9.11” a shekarar 2001, Amurka ta kaddamar da yaki a Afghanistan da sunan “yaki da ta’addanci”. A cikin shekaru 20 da suka wuce, matakan soja da Amurka ta dauka a Afghanistan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, a yayin da wasu sama da dubu 60 suka jikkata. Baya ga haka, kusan kaso 1/3 na al’ummar kasar ta Afghanistan sun kuma zama ‘yan gudun hijira.

Hakan abun takaici ne, kuma abin da ya faru a Afghanistan wani bangare ne kawai na matsalolin da Amurka ta haifar ga sauran kasashen duniya. Bisa sakamakon binciken “Tsadar Yaki” wanda cibiyar Watson mai kula da harkokin kasa da kasa da na al’umma ta jami’ar Brown ta fitar, yakin da Amurka ta kaddamar wai da sunan yaki da ta’addanci cikin shekaru 20, ya haddasa mutuwar mutane sama da 929,000. Ban da wannan, a yayin da ake fuskantar kalubalen annobar Covid-19, Amurka ta yi ta kakkaba takunkumai a kan wasu kasashe, matakin da ya kara tsananta matsalar jin kai da wadannan kasashe ke fuskanta.

Lallai har kullum Amurka na daukar kanta a matsayin misali a wajen kare hakkin bil Adam, amma kuma ga abun da take yi a zahiri.(Mai zane:Mustapha Bulama)