logo

HAUSA

Nahiyar Afrika na duba yuwuwar rage matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa

2022-03-04 10:30:52 CRI

Yayin da ake bikin Ranar Kare Muhalli ta Nahiyar Afrika, masana da hukumomi a nahiyar, sun jaddada bukatar shawo kan annobar da sauyin yanayi ke ci gaba da haifarwa a nahiyar.

A shekarar 2002 ne kungiyar hadin kan Afrika OAU, wadda a yanzu Tarayyar Afrika (AU) ta maye gurbinta, ta ayyana ranar 3 ga watan Maris din kowacce shekara a matsayin Ranar Kare Muhalli ta Nahiyar, a matsayin wata hanya ta wayar da kan jama’a game da kalubalen muhalli da nahiyar ke fuskanta.

Masana sun bayyana cewa, duk da namijin kokarin da ake ci gaba da yi wajen shawo kan tasirin sauyin yanayi, nahiyar na bukatar gaggauta aiwatar da matakai masu karfi domin dakile karuwar kalubalen.

A cewar Adefris Worku, masanin dazuka a hukumar kula da muhalli da dazuka da sauyin yanayi ta Habasha, ana samun karuwar matsalar sauyin yanayi a Afrika saboda abubuwa da dama, cikinsu har da fadada ayyukan gona.

Ana ganin bangaren gona da shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasashen Afrika, a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke janyo kwararar hamada a Afrika. Bisa la’akari da karuwar al’umma, ana kara nome dazuka a fadin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)