logo

HAUSA

Kasar Amurka ce mai kisan kare-dangi

2022-03-04 12:16:14 CRI

A ranar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fidda dogon bayani mai taken “Shaidu game da yadda kasar Amurka ta yi wa mazaunan India kisan kare-dangi”, inda ta fidda cikakkun bayanai da shaidu kan yadda kasar ta yi musu kisan kare-dangi da goge al’adunsu.

Bisa kididdigar da aka yi, daga shekarar 1492 zuwa farkon karni na 20, yawan al’ummomin Indian ya ragu matuka daga miliyan 5 zuwa dubu 250, sabo da raguwar yawan al’umma, Amurka ta tilastawa al’ummomin Indian daidaitawa da goge al’adunsu, lamarin da ya sa, ta kawar musu ’yancin kai baki daya, har ya kai su ga rasa iko wajen raya tattalin arziki. Kuma, gwamnatin Amurka ta hana yaran Indian amfani da harshensu.

Ko da yake, a halin yanzu, kasar Amurka tana ci gaba da nuna fuska biyu kan batun hakkin bil Adama, batutuwan da suka faru cikin tarihinta sun nuna mana cewa, ita ce ta yi wa mazaunan Indian kisan kare-dangi, kuma, bai dace ta kira kanta da “Mai kare hakkin dan Adam” ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)