logo

HAUSA

Tsagaita bude wuta a Sudan ta Kudu na fuskantar koma baya

2022-03-03 10:49:14 CRI

Sabon shugaban rukunin masu sa ido kan batun tsagaita wuta a Sudan ta Kudu Asrat Denero Amad, ya ce tashe tashen hankula dake aukuwa tsakanin alummun jihohin Upper Nile da Unity masu arzikin mai, na haifar da barazana ga burin da ake da shi na tsagaita wuta.

Amad, wanda ya yi tsokacin ga mambobin tawagar masu sa idon jiya Laraba a birnin Juba, ya ce ya damu matuka, game da batun aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a sassan jihohin biyu, duba da yadda wasu ke yiwa tanadin yarjejeniyar kafar ungulu. 

An kafa tawagar sanya ido domin lura da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Sudan ta kudu, mai lakabin COH ne a watan Disambar shekarar 2017.   (Saminu)