logo

HAUSA

Kafar yada labaran Kenya: Kasashen Afirka za su mai da hankali kan taruka biyu na Sin

2022-03-03 14:46:02 CRI

A kwanan nan ne za a fara gudanar da manyan taruka biyu na kasar Sin na bana, kuma a kwanakin baya, kafar rediyo ta kasar Kenya, ta fidda wani rahoto, wanda ya nuna yadda gamayyar kasa da kasa za su ci gaba da mai da matukar hankali kan taruka biyu na kasar Sin.

Rahoton ya nuna cewa, kasar Sin za ta zartas da sabon shirin raya kasa yayin tarukan dake tafe, wanda hakan zai yi muhimmin tasiri kan tattalin arzikin kasa da kasa, gabanin ta kasance a sahun gaba a fannin bunkasuwar harkokin kere-kere cikin kasashen duniya cikin shekaru 12 da suka gabata a jere.

Haka kuma, an ce, taruka biyu na kasar Sin, suna da muhimmanci ga kasashen Afirka, sabo da shugabannin kasashen Afirka suna fatan karfafa dangantakar dake tsakanin kasashensu da kasar Sin, domin raya kasashensu. Kana, a cewar rahoton, duk wanda ke neman bata zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar yada jita-jitar “Tarkon Bashi”, ba zai cimma nasara ba.  (Mai Fassarawa: Maryam Yang)