logo

HAUSA

Birnin Beijing na haskaka ruhin wasannin hunturu na shekarar 2022

2022-03-03 19:30:12 CRI

Bayan kashe wutar gasar Olympic da aka yi a babban filin wasa na “Bird Nest” dake birnin Beijing, sakamakon kawo karshen kasaitacciyar gasar da birnin ya karbi bakuncin ta a bana, ana iya cewa, bukukuwan da suka biyo bayan hakan suna kara nishadantar da al’ummun kasar Sin baki daya.

Bayan gudanar wannan gasa cikin tsawon kwanaki 16, shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa Thomas Bach, ya furta cewa "Bisa ga yadda birnin Beijing ya shirya gagarumar gasar Olympic wadda ta tsere sa’a a shekarar nan ta 2022, muna yiwa Sin maraba da zama kasar wasannin hunturu".

Kasar Sin ta kafa tarihi, na kasancewa wadda ta shirya babbar gasar da aka fi kallon ta a sassan duniya, kuma wadda aka yi amfani da fasahohi na zamani yayin gudanar da ita, yayin da birnin Beijing ya kara fitar da tasirin sa a rayuwa ta zahiri, inda karin masu wasannin hunturu suka shiga gasar da ta gudana, kana kasuwar masana’antun wasannin kankara ma ta bunkasa, baya ga yadda zuwan gasar ya dasa wani iri na kaunar wasannin hunturu a zukatan miliyoyin al’ummar Sinawa.

A cewar kakakin kwamitin IOC Mark Adams, ya zuwa ranar 11 ga watan Fabarairun daya shude, cikin kasar Sin, an kalli gasar Olympics ta birnin Beijing ta kafar talabijin na tsawon sa’oi biliyan 2.05, adadin da ya haura jimillar kallon da aka yiwa gasannin birnin PyeongChang a shekarar 2018, da ta birnin Sochi a shekarar 2014, da kaso 15 bisa dari.

Cikin wadanda suka kalli gasar akwai Li Yunxi da kanwarta Li Yunting, yara ne ‘yan firamare dake karatu a birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin. Lokacin da ake nuna wannan gasa yayin da suke hutun makaranta, yaran sun nacewa kallon wasan zamiyar kankara na “roller skating” ta kafar talabijin.

A ranar 5 ga watan Fabarairu, yaran tare da mahaifin su Li Xiang, sun kalli yadda a karon farko a tarihi, kasar Sin ta samu nasarar lashe lambar zinari ta tseren zamiyar kankara. Li Xiang ya ce "sun yi matukar farin ciki, har sun nemi damar gwada wasan zamiyar kankara na “ice skating”. Magidancin ya fadi hakan ne, yayin da ya raka yaran na sa zuwa bikin wasan kankara na Wuhan, wanda aka bude ga al’umma kyauta.

A duk sassan duniya, gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing, ta zamo a sahun gaba wajen yawan ‘yan kallo, inda sama da Amurkawa miliyan 100 suka kalli wasan ta kafar NBCUniversal.

Kari kan masu kallo ta talabijin, akwai kuma masu sha’awar wasannin da suka bibiye shi ta kafafen sada zumunta, inda kafafen suka samu mabiya biliyan 2.7, matakin da ya sanya gasar samun mabiya mafi yawa a tarihin gasannin hunturu da aka taba gudanarwa a baya.

A dandalin sada zumunta na Weibo na kasar Sin, wanda ke kama da shafin Tiwita, adadin tattaunawar da ake yi game da gasar ta birnin Beijing ta shekarar 2022, sun kai sama da rabin dukkanin tattaunawa 50 mafi jan hankalin jama’a tun bayan bude gasar. ‘Yan wasa da suka yi nasarar lashe lambobin yabo da ma, wadanda ba su yi nasara ba sun samu kauna daga ‘yan kallo.

‘Yar wasan zamiya ta kasar Sin Gu Ailing, ta samu karin sabbin mabiya sama da miliyan 2.86 a shafin ta na Weibo cikin mako guda, yayin da mabiyan dan wasan “short-track skating” Wu Dajing, suka zarce miliyan 10, bayan ya yi nasarar samun matsayi na 5 a ajin maza na gudun zamiyar kankara na mita 5,000, a wannan lokaci da yake ban kwana da Olympics da ta gudana a kasar sa.

A harabar dandalin, masu sha’awar wasanni na karuwa sosai. Wasu alkaluma daga shafin yanar gizo na kamfanin Ctrip mai shirya tafiye tafiye sun nuna cewa, adadin masu kama otal otal dake kusa da wuraren yin wasan “skiing” sun karu da kaso 54 bisa dari a shekara guda, yayin da bukatar tikitin yankunan da ake wasannin hunturu suka karu da kaso 40 bisa dari sama da na shekarar bara.

Kaza lika wasu alkaluma sun nuna yadda mazauna birnin Beijing, birnin da ya karbi bakuncin gasar Olympics ta bana, suka rika yawaita duba ma’anar gasannin hunturu, kamar "skiing" da kalmomin Kankara da dusar kankara a shafin Mafengwo, shafin sada zumanta mai shirya tafiye tafiye, kana masu neman sani kan wadannan kalmomi suka karu da kaso 215 bisa dari, a yayin bikin bazana na bana da ya gabata. Har ila yau a birnin Wuhan, wanda aka fi sani da "Birnin Dumi", mutane na yin layi tsawon lokaci kafin samun damar shiga zauren wasan zamiyar skating na kankara.

A cewar manajan cibiyar wasannin kankara ta birnin Wu Linli, bayan bude gasar ta bana, adadin masu zuwa shiga wasan ya ninka sau 3, yayin da masu neman shiga kwas domin koyon wasannin suka ninka sau biyu.

Ita ma kungiyar wasannin kankara da dusar kankara ta Wuhan, ta ce dukkanin cibiyoyi 8 na wasan kankara dake Wuhan suna cika makil. Kaza lika alkaluma sun nuna yadda yankin gandun daji na Shennongjia dake yammacin lardin Hubei, ya samu karin masu zuwa bude ido da sama da tafiye tafiye 70,000, inda mahalartan sa ke zuwa yin wasan skiing tun daga ranar 1 ga watan Fabarairun nan kawo yanzu.

A dukkanin fadin kasar Sin, an samu karuwar tafiye tafiye na bude ido masu nasaba da kankara da dusar kankara, daga miliyan 170 tsakanin shekarun 2016 zuwa 2017, zuwa miliyan 254 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021, ana kuma hasashen adadin na iya karuwa zuwa miliyan 305 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022, kamar dai yadda wani rahoto na hukumar lura da yawon shakatawa da shafin Mafengwo ya nuna.

Babban burin dake tattare da dukkanin gasannin da kasar Sin ke shiryawa shi ne jan hankalin karin Sinawa zuwa ga wasanni. A shekarar 2015, Sin ta tsayar da manufar shigar da karin Sinawa miliyan 300 cikin wasannin hunturu, lokacin da birnin Beijing ya samu izinin karbar bakuncin gasar Olympics ta 2022. Tun daga lokacin ne kuma, aka samu karin dandazon gine ginen ababen more rayuwa masu nasaba da wasannin hnuturu a kasar Sin.

A yanzu haka, Sin na da manyan zaurukan wasan kankara 654, adadin da ya karu da kaso 317 daga shekarar 2015 zuwa yanzu, yayin da kuma wuraren wasan skiing suka karu daga 568 a shekarar 2015 zuwa 803 a yanzu. Ya zuwa watan Oktoba na shekarar 2021, sama da mutane miliyan 346, kusan kaso 1 bisa 4 na al’ummar Sinawa sun taba shiga wani bangare na harkokin da suka shafi wasannin hunturu.

Game da hakan, daraktan watsa labarai na babbar hukumar shirya wasanni ta kasar Sin Tu Xiaodong, ya ce cika wannan alkawari shi ne babban abun bajimta, wanda gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing ta 2022 ta samar ga duniya. Ana iya cewa, wannan tamkar wata lambar zinari ce irinta ta farko ga birnin Beijing.

Tun daga gasar Olympics ta shekarar 2008 da ya karbi bakunci, birnin Beijing ya sauya kirarinsa daga "Fatan bunkasa wasanni " zuwa nasarori na zahiri, inda aka gina tarin wuraren motsa jiki, aka kuma bunkasa bincike da koyar da kimiyyar wasanni daban daban, yayin da kuma ake fadada adadin gasanni da ake gudanarwa a sassan kasar ta Sin.

Kusan dukkanin unguwanni ko makarantu a Sin, suna da a kalla wurin wasan kwallon tebur daya, yayin da sauran wasanni, kamar iyo, da  badminton, da taekwondo, ke da miliyoyin masu yin su.

Har yanzu dai ana sa ran ganin karin tasirin gasar Beijing ta 2022, a fannin karuwar adadin masu shiga wasanni daban daban na hunturu. Ana iya cewa, gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022 tamkar iri ne da aka shuka a Sin. Wanda nan gaba kadan, zai haifar da karuwar adadin masu shiga a dama da su a wasannin hunturu, da hasashen adadin kimanin mutum miliyan 500 ko fiye, kuma wasannin hunturu za su zama jini da tsoka a rayuwar Sinawa.