Wasu ilmi kan taron NPC da na CPPCC na kasar Sin
2022-03-02 09:06:33 CRI
Yanzu haka ’yan kwanaki suka rage a fara taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice sai kuma majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin NPC na shekarar 2022 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda majalisun za su tattauna batutuwan da suka shafi makomar kasar Sin baki daya.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC), majalisa ce da ta kunshi mambobi daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da jam'iyyun siyasa, kungiyoyi da wakilai masu zaman kansu da sauransu. Kuma bisa al'ada, jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ce ke da wakilai mafi rinjaye a majalisar, inda take da kashi 1 bisa 3 na daukacin mambobin majalisar. Sauran mambobin majalisar sun fito ne daga jam'iyyun da ke kawance da jam'iyyar kwaminis mai mulki da sauran wakilai masu zaman kansu wadanda ba sa cikin kowace jami'yya.
Ita kuma majalisar wakilan jama'a wato NPC a takaice, majalisa ce da ake zaben wakilanta daga mazabun gundumomin kasar, yankuna masu cin gashin kansu, birane dake karkashin kulawar gwamnatin tsakiya, rundunar sojojin kasar da sauransu.
Aikin majalisar wakilan, sun hada da gyaran kundin tsarin mulkin kasa da sanya ido wajen ganin an aiwatar da tanade-tanaden da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar, kafa dokoki da suka shafi manyan laifuffuka, harkokin jama'a, hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran batutuwan da suka shafi rayuwar Sinawa.
Har ila yau, majalisar wakilan ce take zabe da kuma nada wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati da yanke hukunci game da manyan batutuwan da suka shafi kasa baki daya.
Masana na bayyana cewa, kamar yadda aka saba, a tarukan na bana ma, ana sa ran za a tattauna muhimman batutuwa kamar, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki, da matakan inganta rayuwar al'umma, da manufofin diflomasiyar kasar Sin, da batun mamakshi mai tsafta da nasarorin da kasar ta cimma wajen shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing na shekarar 2022 da ajin nasakassun da ake shirin farawa, da sauran muhimman batutuwa da suka shafi kasar da matakan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)