logo

HAUSA

Sudan ta kudu da bakin duniya da UNICEF sun kaddamar da gangamin bunkasa kiwon lafiya

2022-03-02 11:42:39 CRI

Maaikatar lafiyar kasar Sudan ta kudu, da bankin duniya, da kuma hukumar UNICEF, sun kaddamar da wani shiri a ranar Talata, na gangamin wayar da kai game da shirin hadin gwiwar kiwon lafiya da kuma wayar da kai a tsakanin bangarorin dake kawance game da yadda za a kara zuba jari a fannin kiwon lafiya.

Za a gudanar da gangamin ne a tsawon watan Maris, kana za a yi amfani da dukkan bangarorin kafafen yada labarai da hanyoyin isar da sakonni game da shirin hidimomin kiwon lafiya na hadin gwiwa inda za a yada bayanan ta hanyar manyan alluna, da bidiyo, da kuma hanyoyin fadakarwa ga alumma.

Hukumar UNICEF ta bayyana cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a Juba, babban birnin kasar Sudan ta kudu cewa, shirin gangamin fadakar da alummar zai mayar da hankali wajen bayyana muhimmancin taka rawa a ayyukan kiwon lafiya daban-daban, da suka hada da gangamin alluran riga-kafi, da riga-kafin yaki da COVID-19. (Ahmad)