logo

HAUSA

Mike Pompeo Ya Ziyarci Taiwan Ne Da Mugun Nufi

2022-03-02 21:41:39 CRI

Yau ne, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin tare da mugun nufinsa, wanda kullum yake yunkurin zama shugaban Amurka. Nufin Mike Pompeo na ziyartar Taiwan a wannan karo, shi ne domin neman samun goyon bayan masu adawa da kasar Sin a Amurka da kuma karfafa tasirinsa. Kwana guda kafin Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan, gwamnatin Amurka ta aika da wata tawaga mai kunshe da tsoffin jami’an tsaron kasa zuwa Taiwan, lamarin da ya nuna cewa, dukkan jam’iyyun siyasar Amurka wadanda suka yi mulki ko ba su yi mulki a kasar ba, sun mayar da Taiwan a matsayin wani wuri da zai ba su ribar siyasa da kuma samun kuri’u.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya. Ba wanda zai iya raba Taiwan daga kasar Sin. Dole a dinki kasar Sin baki daya, kuma tabbas za a dinki kasar Sin baki daya, lamarin da ba za a dakatar da shi ba. Yunkurin nuna wa Taiwan goyon bayan da wasu Amurkawa suka yi ta hanyar ziyartar yankin, ba zai samu nasara ba. Kamata ya yi Amurka ta martaba manufar “kasar Sin daya tak a duniya” da sanarwa guda 3 ta hadin gwiwar Sin da Amurka, ta daina kau da kai kan batun neman ‘yancin kan Taiwan da kuma goyon bayan aikace-aikacen, ta kuma dakatar da kulla makarkashiyar hana ci gaban kasar Sin bisa hujjar batun Taiwan. Don haka, bai kamata a kaskantar da aniyar al’ummar kasar Sin da kwarewarsu ta kiyaye ikon mulkin kasa da kuma cikakken yankunan kasa ba. (Tasallah Yuan)