logo

HAUSA

Najeriya ta sha alwashin kara kaimi wajen yaki da satar mutane da hargitsa makarantu

2022-03-02 19:10:50 CRI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ana kara zage damtse wajen tunkarar matsalar sace-sacen mutane da lalata makarantu a fadin kasar.

Buhari ya bayyana haka ne yayin taron karawa juna sani kan harkokin tsaron kasa a Abuja, babban birnin kasar jiya Talata. Ya bayyana cewa, gwamnati ba za ta sake lamuntar yadda yan ta’adda da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kawo tarnaki ga tsarin ilimi da harkokin tattalin arzikin kasa ba

Ya ce, har yanzu batun samar da tsaro ga Najeriya da ‘yan Najeriya baki daya, shi ne babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba, kuma gwamnati za ta ci gaba da gina tattalin arziki mai inganci da dorewa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da kokarin samar da ingantaccen ilimi, da inganta zamantakewar jama'a, da samar da ingantattun ababen more rayuwa.

Ya kuma yabawa hukumomin tsaro, kan kokarin da suke yi na magance ayyukan ta’addanci, da tayar da kayar baya, da ‘yan fashi da makami da sauran matsalolin tsaro a sassan kasar. (Ibrahim)