logo

HAUSA

Ana Wata Ga Wata…

2022-03-02 17:05:03 CRI

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda hukumomi da masana a fannin yaki da sauyin yanayi, na yin gargadi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana maganar “targade sai ga karaya”. Masana sun sha yin kashedi tun kafin annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba ganin irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.  

Amma duk da wannan babbar matsala da aka yi hasashen za ta kunno kai, masana sun sha fadawa zaman muhawarar kwamitin sulhun MDD a lokuta daban-daban kan yadda za a kare fararen hula da yunwa ta shafa sakamakon rikici cewa, yayin da ake fama da COVID-19, ba kawai muna fama da annobar lafiya da ta shafi duniya baki daya ba, har ma ta haifar matsalar jin kai."

Wasu alkaluman da aka fitar game da matsalar abinci da duniya ke fuskanta, na nuna cewa, kimanin sama da mutane miliyan 800 ne suke kwana da yunwa a duniya. Akwai kuma karin sama da mutane miliyan 100 dake fama da matsalar yanayi na yunwa ko fiye da haka.

Wannan ya sa kwararru, yayin taron kaddamar da rahoto na 6 na sassan gwamnatocin nahiyar da ya gudana a Nairobin Kenya game da sauyin yanayi ko IPCC a takaice, taron da ya gudana a gefen ci gaban taron dandali na 5, na hukumar MDD mai lura da muhalli ko UNEA-5, bukatar samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan dakile tasirin sauyin yanayi tun daga tushe, domin baiwa nahiyar damar jurewa alamun sauyin yanayi kamar fari, da karuwar zafi, da wutar daji, tare da yaduwar cututtukar da wasu halittu ke bazawa.

Kwararrun na ganin cewa, cimma nasarar kafa tsarin da zai baiwa nahiyar Afirka damar jure mummunan tasirin sauyin yanayi, da muhalli mai inganci, ya dogara ne ga nasarar samar da isassun kudaden gudanar da muhimman ayyuka masu nasaba da hakan.

Baya ga matsaloli na rashin abinci sakamakon matsalar sauyin yanayi, hukumomin kudi irinsu Bankin Duniya ya yi hasashen cewa, za a samu raguwar kudade a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, sakamakon matsalar tattalin arziki da cutar COVID-19 ta haifar gami da rufe wuraren ayyukan yi.

Sai dai, duk da hasashen da bankin ya yi na kaso 4 cikin 100 na al'amura za su farfado a shekarar 2021 da ta gabata, a hannu guda kuma, al'amura za su sake komawa baya, saboda raguwar kudaden shiga da ayyukan yi da ma'aikata 'yan ci-rani za su fuskanta, matakin da zai kara haifar da rasa ayyukan yi da kudin shiga sakamakon matsalar tattalin arziki a kasashen da suke zama.

Yayin da duniya ke kara koyon darussa da dama daga COVID-19, da sauran bala’u daga indallahi, hakika lokaci ya yi da za a karkata ga tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato gina kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, don samun duniyar da kowa zai ji dadin zama a cikinta cikin kwanciyar hankali da walwala. (Ibrahim Yaya)