logo

HAUSA

Kenya na fatan jan hankalin kasashen da ba sa kusa da teku su ci gajiya daga tashar ruwan Lamu

2022-03-02 10:09:25 CRI

Mahunkun kasar Kenya, sun sha alwashin baiwa kasashe makwaftanta damar amfana daga tashar tekun ta dake Lamu, domin raya tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa.

A jiya Talata, babban darakta, kuma shugaban hukumar raya hada hada a yankunan tashar Lamu da Sudan ta kudu da Habasha ko LAPSSET, Mr. Stephen Ikua, ya shaidawa mahalarta wani taron wakilan nahiya da ya gudana a birnin Nairobi cewa, tashar Lamu wadda ita ce tashar ruwa ta biyu ta hada hadar sufurin ruwa a Kenya, na iya karbar manyan jiragen ruwa irin wadanda tashar Mombasa ke karba saboda zurfinta.

Yayin taron mako guda, karo na 7, game da raya ababen more rayuwa a Afirka ko PIDA a takaice, wanda hukumar NEPAD ta shirya, Mr. Ikua ya ce kasar Sudan ta kudu mai tarin albarkatun kasa da na noma, za ta iya amfani da tashar Lamu, wajen fitar da albarkatun ta zuwa ketare, don bunkasa kudaden shigarta, maimakon dogaro da cinikayyar danyen mai kadai. 

A watan Mayun shekarar 2021 da ta gabata ne shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya kaddamar da fara aiki da sashen farko na tashar Lamu a hukumance.  (Saminu)