logo

HAUSA

Dabarar Kawar Da Matsala Sun Nuna Yadda Ake Samun Kauna Tsakanin Al’umma

2022-03-01 17:33:00 CMG

Sharhi daga Bello Wang

Nan da ‘yan kwanaki za a kaddamar da wasannin Olympics ajin nakasassu na lokacin hunturu a birnin Beijing na kasar Sin, inda kasar ta dau niyyar samar da wani yanayi na kawar da duk matsaloli ga dukkan ‘yan wasa nakasassu na kasashe daban daban.


A cikin wuraren cin abinci da aka gina wa ‘yan wasan, ana iya daidaita tsayin teburori, ta yadda ‘yan wasa masu yin amfani da keken guragu za su iya debo abinci, da cinsu cikin sauki. Sa’an nan a dakunan kwanansu, an daidaita tsare-tsaren kayayyaki, ta yadda makafi ba za ci karo da wani abu su ji raunuka ba.

Ba don wasannin Olympics kawai ake samar da wadannan tsare-tsare na musamman ba. Idan ka kewaya a titunan Beijing, za a ga kayayyakin na musamman na saukakawa nakasassu. Misali, hanyar da aka kebe wa makafi, da fitilun da suke iya samar da murya don taimakon makafi tsallake hanya, da dai sauransu.

Ban da kayayyaki, don samar da wani yanayi na kawar da matsala ga nakasassu, ana bukatar samun taimako daga gwamnati da sassan al’umma. Misali, a nan birnin Beijing, hukuma ta hada aikin samar da guraben aikin yi ga nakasassu, da kare fasahohin al’adun gargajiya a waje guda. Inda na ga wasu dimbin nakasassu da suka kama ayyukan sarrafa kayayyakin al’adu da hannu. Ban da wannan kuma, na ga wani nau’in sinima da aka bude wa makafi, inda ake yi musu bayani yayin da ake haska fina-finai. Duk wadannan abubuwa daban daban suna taka muhimmiyar rawa, a kokarin samar da wani muhalli na kawar da matsalar zaman rayuwa ga nakasassu.

Na kan tuna da wata tambaya: Shin nakasassu ne kadai suke bukatar wani muhalli mai sauki? Hakika duk wani mutum daga cikin mu na iya fuskantar wata matsala. Misali, bayan da muka tsufa, ko kuma lokacin da muka ji rauni, mu kan bukaci samun taimako daga sauran mutane. Saboda haka, aikin nan na samar da wani muhalli maras matsala, wani kokari ne na kyautata ayyukan kula da al’umma, ta yadda dukkan mutane za su samu saukin zama, da jin dadin zaman rayuwa. Wannan aiki yana ba da tabbaci ga zaman rayuwar nakasassu, gami da tabbatar da ci gaban al’ummar dan Adam.   (Bello Wang)