Abdulsalam Sufi: Ina kira ga daliban Najeriya da su koyo ilimi daga kasar Sin don taimakawa ci gaban kasarsu
2022-03-01 17:01:24 CRI
Abdulsalam Sufi, dan asalin jihar Kano ne a tarayyar Najeriya, wanda ya shafe kusan shekaru 9 yana karatu a kasar Sin, musamman birnin Beijing. Bayan da ya gama karatu ya koma kasarsa, ya taba aiki tare da wasu kamfanonin kasar Sin dake wurin. Yanzu Sufi ya zama dan kasuwa wanda ya bude kamfanin kansa.
A zantawar da ya yi da Murtala Zhang kwanan nan, Abdulsalam Sufi ya bayyana ra’ayinsa, kan bambancin yanayin karatu tsakanin kasar Sin da Najeriya, da kuma yadda yake ganin wasu jita-jitar da wasu kafafen watsa labaran kasashen yamma ke yadawa game da kasar Sin.
A karshe, Sufi ya yi kira ga daliban Najeriya da har yanzu suke karatu a kasar Sin, da su kara kokarin karatu don koyo ilimi na gina kasarsu. (Murtala Zhang)